Tsige Yan Majalisar PDP 23: Gwamnan Filato Ya Ziyarci Tinubu, Ya Yi Karin Bayani
- Gwamnan jihar Filato ya nuna damuwa kan makomar yan majalisar dokokin jihar Filato da aka tsige daga kujerunsu
- Bayan ya gana da Tinubu a Villa, Gwamna Caleb Mutfwang ya ce za a binciko duk hanyoyin da za a iya magance lamarin, ta fuskar siyasa da doka
- Mutfwang ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da ganin cewa zaman lafiya ya dawo jihar Filato kuma za a kashe wutar rikicin siyasar da ke kara ruruwa
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ce suna shirye shiryen bin hanyoyin da suka dace wajen kawo karshen rikice-rikicen da suka jawo aka sauke wasu yan majalisa na jihar.
Gwamnan Mutfwang ya ce daga cikin hanyoyin da za su bi sun hada da na doka da kuma ta siyasa, rahoton The Nation.
A watan Nuwambar 2023 ne kotun daukaka kara ta yanke hukuncin tsige yan majalisun jihar 16, wadanda suka hada da na jiha da tarayya, da kuma sanatoci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gaba daya wadannan yan majalisar sun kasance mambobin jam'iyyar PDP, lamarin da ya jefa jam'iyyar cikin wani yanayi.
A halin da ake ciki, majalisar dokokin jihar za ta dawo zama a mako mai zuwa cike da fargabar cewa, watakila mambobin jam'iyyar PDP takwas da suka rage bayan kotun daukaka kara ta tsige sauran su ki rantsar da sabbin mambobin kasancewar sun cike sharudda.
Da yake martani kan ci gaban, Gwamna Mutfwang, a yayin ziyarar da ya kai fadar shugaban kasa Abuja, ya ce ana duba dukkan hanyoyin da za a bi, rahoton Premium Times.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa ya kai ziyarar godiya ne ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a Villa, kan kin tsoma baki a harkokin shari'a.
Hakan na zuwa ne bayan nasarar da ya samu a Kotun Koli a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu wacce ta soke hukuncin tsige shi tare da tabbatar da shi a matsayin halastaccen gwamnan Filato.
Mutfwang ya magantu kan ganawarsa da Tinubu
Da aka tambaye shi kan dalilinsa na zuwa Villa, Mutfwang ya ce:
"Na zo ganin shugaban kasar musamman don na yi babban godiya ga mai girma shugaban kasa, kan raya damokradiyya a Najeriya."
Yadda APC ta ci banza a Filato
A baya mun ji cewa kotun daukaka kara ta tsige gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang da duka ‘yan majalisan da aka zaba a karkashin PDP a bara.
Amma da aka je kotun koli, sai ga shi alkalai sun dawo da Mai girma Caleb Mutfwang a mulki, aka rusa hukucin da aka yi a baya.
Asali: Legit.ng