Sheikh Bala Lau ya yabawa Uba Sani kan 'inganta walwalar' mazauna Kaduna
Abdullahi Bala Lau, shugaban kungiyar Izalatil Bida wa Ikamatus Sunnah (JIBWIS) na kasa, ya jinjinawa Uba Sani, gwamnan jihar Kaduna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Da ya ke jawabi a wurin gasar karatun Al-Kurani mai girma a Kinkinau a Kaduna, Bala Lau ya ce Uba Sani ya nuna cewa ya damu da inganta rayuwar yan jihar Kaduna ta hanyar bulo da shirye shirye da dama.
Gwamnan na Jihar Kaduna ya bada kyautan kudi da kyaututuka a matakai daban-daban na gasar, The Cable ta rahoto.
Gwamnan ya ce:
"Mutane biyu cikin da suka zo na farko daga bangaren mata da maza duk za a basu kujerar aikin hajji na shekarar 2024".
Sani ya yi kira ga wadanda suka fafata a gasar su rika amfani da darrusan da suka koya cikin AlKurani a rayuwarsu na yau da kullum.
Ya yi kira ga musulmi "su rungumi koyarwa da shiriya da ke Alkur'ani, saboda babban tasirin da ya ke da shi a dukkan bangarorin rayuwarsu."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya ce an kafa kwamiti da za ta duba kallubalen da aka fuskanta yayin aikin hajji na bara da nufin magance su.
Ya bayyana bacin ransa kan wasu abubuwa marasa dadi da aka fuskanta yayin aikin hajjin na shekarar da ta gabata.
Sani ya kuma yi gargadi ga mutanen da suka same shi da cewa a basu kwangilar samarwa maniyyata abinci, yana mai cewa duk wanda ya cuci maniyyata zai janyowa kansa fushin Allah domin addu'ar wanda aka zalunta tana isa ga Allah ba tare da shamaki ba.
Dakaci karin bayani
Asali: Legit.ng