NNPP Ta Aika Sako Ga NJC Kan Hukuncin Kotun Daukaka Kara Na Korar Gwamna Abba Na Kano
- Jam'iyyar NNPP ta yi kira ga majalisar alkalai da ta bankado kulle-kulle da sabanin da ke tattare da kwafin takardar CTC na hukuncin kotun daukaka kara
- Hukuncin da kwamitin mutum uku karkashin mai shari'a Moore Adumien ya yanke a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2023, na ci gaba da haifar da martani
- Legit Hausa ta rahoto cewa takardar CTC na hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke wanda aka saki a ranar Talata ya zo da sabanin tsige Gwamna Abba Yusuf
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Kano, jihar Kano - Shugabancin jam'iyyar NNPP ya yi kira ga majalisar alkalai ta kasa da ta binciki takaddamar da ke kewaye da hukuncin kotun daukaka kara kan rikicin zaben gwamnan jihar Kano.
Legit Hausa ta tuna cewa hukuncin kotun daukaka karar wanda ya tabbatar da tsige Gwamna Abba Yusuf, ya haifar da zafafan martani a fadin Najeriya, rahoton The Nation.
NNPP ta bukaci majalisar alkalai ta binciki takardar CTC
A ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, kwamitin aiki na jam'iyyar NNPP ya yi kira ga majalisar alkalai da ta fara bincike kan hukuncin yayin da lamarin siyasar na Kano ke ci gaba da jan hankalin yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, sakataren NNPP na kasa, Dipo Olayioku, wanda ya wakilci mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa Abba Kawu Ali, ya bayyana cewa kwafin takardar CTC da lauyoyin jam'iyyar suka samu ya nuna karara cewa hukuncin da kotun daukaka karar ya kai nasara ga Gwamna Yusuf.
Jaridar Guardian ma ta tabbatar da matsayin jam'iyyar NNPP.
Yanzun nan: Kotun Daukaka Kara ta magantu kan hukuncin zaben gwamnan Kano, tace an samu kuskure a takardar CTC
Olayioku ya ce:
"Muna kira ga majalisar alkalai, da ta fara bincike ba tare da bata lokaci ba don gano abun da ya faru a cikin lamarin.
"Bugu da kari muna kira ga shugabanni, dattawa da sauran manyan masu ruwa da tsaki a aikin Najeriya, ciki harda kafofin watsa labarai, da su shiga cikin lamarin domin dakile hatsarin da irin wannan zai haifar musamman ga damokradiyyarmu da kasarmu gaba daya."
An yi zanga-zanga a Kano
A wani labarin, mun ji cewa magoya bayan jam'iyyar NNPP sun mamaye titunan jihar Kano a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, domin yin zanga-zanga kan kayen da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha a kotun daukaka kara.
Daga bisani jami’an yan sandan Najeriya sun tarwatsa masu zanga-zangar ta hanyar harba barkonon tsohuwa.
Asali: Legit.ng