“Muna Ta Addu’a”: Ta Hannun Damar Ganduje Ta Yi Martani Ga Hukuncin Kotu da Ta Tsige Abba Gida Gida

“Muna Ta Addu’a”: Ta Hannun Damar Ganduje Ta Yi Martani Ga Hukuncin Kotu da Ta Tsige Abba Gida Gida

  • Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja, ta soke zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba
  • Kotun daukaka karar ta riki cewa jam'iyyar NNPP ta take kundin tsarin mulki ta hanyar daukar nauyin Abba, wanda ba dan jam'iyyar bane
  • Bayan hukuncin, ministar Tinubu, Mariya Mahmoud, ta nuna farin cikinta sannan ta taya dan takarar gwamnan APC a jihar Kano, Nasir Gawuna murna

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Mariya Mahmoud, karamar ministar babban birnin tarayya, ta nuna farin cikinta da hukuncin kotun daukaka kara wacce ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.

A cewar Mariya, "Mun dade muna addu'a akan wannan hukunci".

Kara karanta wannan

Jigon NNPP ya yi zazzafan martani kan hukuncin kotun daukaka kara na sauke Abba Gida-Gida

Mariya Mahmoud ta taya Gawuna murnar nasara kan Abba a kotun daukaka kara
“Muna Ta Addu’a”: Ta Hannun Damar Ganduje Ta Yi Martani Ga Hukuncin Kotu da Ta Tsige Abba Gida Gida Hoto: Terfa Naswem, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Minista ya taya Gawuna murna kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke

Ministar ta yi godiya ga Allah kan hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohuwar kwamishinan ilimin ta jihar Kano ta yi rubuce-rubuce a shafukanta na dandalin soshiyal midiya a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba.

“Ina taya dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar APC, Dr. Nasir Gawuna da abokin takararsa Murtala Garo murnar nasarar da suka samu a kotun daukaka kara da safiyar yau.
“Mun dade muna addu’ar samun wannan hukunci, kuma Allah (SHW) ya amsa hukuncin da ya bayyana dan takararmu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jiharmu mai albarka.
"Alhamdullilahi! Alhamdullilahi! Alhamdullilahi!"

Legit Hausa ta rahoto cewa Mariya ta kasance yar hannun damar Abdullahi Umaru Ganduje, shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun daukaka kara: Farfesan arewa ya yi gargadi kan yiwuwar barkewar rikici a Kano

A siyasa, Ganduje shine babban abokin hamayyar Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano.

Ganduje shine gwamnan jihar Kano da ya mika mulki, yayin da na hannun damar Kwankwaso, Abba, ya kasance wanda ke rike da shugabanci a jihar ta arewa maso yamma kuma jigon NNPP.

Mamban APC kuma mazaunin unguwar Mile 9 da ke cikin birnin Kano, Aminu Suleiman, ya ce ba wai ƴaƴan APC ba kaɗai, har wasu mambobin NNPP suna fatan Abba ya sauka.

Ɗan siyasan ya shaida wa Legit Hausa cewa akwai kanawa da yawa da sun zaɓi NNPP, amma rusau ɗin da aka yi da wasu dalilai ya sa sun yi nadamar zaɓen Abba.

"Fatan mu kotun koli ta tabbatar da wannan hukuncin. bari na faɗa ma gaskiya, mu ke zaune a Kano, muna tare da waɗanda suka zaɓi NNPP, ina tabbatar maka sun yi nadama."

Dalilin da yasa kotu ta tsige Abba

Kara karanta wannan

"Yan maula sun fara": Jama’a sun yi caaa kan Ali Nuhu bayan ya taya Gawuna murnar nasara a kotun

A gefe guda, mun kawo a baya cewa a yau Jumu'a, 17 ga watan Nuwamba, 2023 Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a birnin tarayya Abuja ta sauke Abba Kabir Yusuf daga kujerar gwamnan jihar Kano.

Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar Nasir Gawuna na jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel