INEC Ta Dage Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Bayelsa, Cikekken Bayani Ya Bayyana
- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta dage zaman ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bayelsa
- Za a dawo da ci gaba da kidaya da karfe 3:00 na yammaci Lahadi, 12 ga watan Nuwamba
- Ana fafatawa a zaben tsakanin gwamna mai ci, Duoye Diri da wasu yan takara 15
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Yenagoa, jihar Bayelsa - Bayan ayyana sakamakon zabe a kananan hukumomi uku na jihar Bayelsa, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta dage ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna zuwa karfe 3 na yammacin ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba.
Baturen zaben, Farfesa Faruk Kuta, ne ya sanar da hakan yayin da yan Najeriya suka zuba idanu cike da zullumi don sanin wanda zai lashe zaben gwamnan na jihar Bayelsa na 2023.
Jaridar Vanguard ce ta sanar da wannan ci gaban a cikin wata wallafa da ta yi a shafinta na dandalin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A halin da ake ciki, dan takarar PDP kuma gwamna mai ci, Duoye Diri, ne kan gaba a zaben da kuri'u 38,403, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.
Channels TV ta rahoto cewa har yanzu ana jiran sakamakon zabe daga kananan hukumomi biyar.
Duoye Diri ya lashe karamar hukumarsa
Da farko Legit Hausa ta rahoto cewa jam’iyyar PDP a jihar Bayelsa ta samu gagarumar nasara ta farko a karamar hukumar gwamnan jihar kuma dan takarar gwamna, Douye Diri.
Yayin da APC ta samu kuri'u 5,349, jam'iyyar Labour Party (LP) ta samu kuri'u 22. A halin da ake ciki, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta fara tattara sakamakon karshe a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa kuma nan ba da dadewa ba za a sanar da wanda ya lashe zaben.
Ya takara da jam'iyyun siyasa 16 ne suka yi takara a zaben gwamnan na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Gwamna mai ci kuma dan takarar PDP, Diri wanda ke neman zarcewa kan kujerarsa ya fafata da yan takara 15 ciki harda Timipre Sylva na APC da Udengs Eradiri na jam'iyyar LP.
Asali: Legit.ng