Ganduje Ya Caccaki Kwankwasiyya Wajen Yi wa Shugabannin NNPP Wankar Shiga APC

Ganduje Ya Caccaki Kwankwasiyya Wajen Yi wa Shugabannin NNPP Wankar Shiga APC

  • Dr Abdullahi Umar Ganduje ya karbi tsofaffin ‘ya ‘yan jam’iyyun PDP da NNPP da su ka shigo jam’iyyar APC mai ci
  • Shugaban APC na kasa ya yi amfani da damar wajen sukar tafiyar babban abokin gabansa, Rabiu Musa Kwankwaso
  • Ganduje ya zargi mabiya darikar Kwankwasiyya da gurbata jam’iyyar NNPP, ya ce za a dama da sababbin shigan a APC

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya karbi wasu tsofaffin shugabannin NNPP da su ka canza gida a siyasa.

Daily Trust ta ce Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa Farfesa Rufai Ahmed Alkali da wasu mutanensa maraba da shigowa APC mai mulkin kasa.

Jam'iyyar NNPP ta rasa jagororinta zuwa APC

Kara karanta wannan

Tarnaki a NNPP yayin da tsohon ciyaman din jam'iyya na kasa da dan takarar gwamna suka koma APC

Tare da Rufai Alkali wanda ya rike NNPP a matakin kasa akwai tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar da ‘dan takaran Gwamnan jihar Kaduna.

Abdullahi Umar Ganduje OFR
Shugaban APC ya karbi 'Yan NNPP Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika akwai Farfesa Bem Angwe wanda ya yi wa NNPP takarar gwamna a Benuwai kuma kafin nan shi ne mai bada shawara kan shari’a.

Ragowar sun hada da manyan ‘yan siyasa da su ka fice daga jam’iyyar ta NNPP da PDP.

Meyasa 'Yan NNPP su ka dawo Jam'iyyar APC?

Yayin da ya ke jawabi a madadin sauran wadanda su ka shigo tafiyar jam’iyya mai mulki, Farfesa Rufai Alkali ya ce ba kwadayi ya kawo su ba.

An rahoto Farfesan ya na cewa muddin ‘dan siyasa ya na son cigaba, dole ya bi APC, ya na mai yabawa salon mulkin Dr. Ganduje da Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Ganduje da gaske yake, jam'iyyar APC ta ƙara yi wa PDP da wasu jam'iyyu 3 Babban Lahani a Arewa

Ganduje ya tabo 'Yan Kwankwasiyya

Shi kuwa Dr. Ganduje da ya tashi magana, ya yi maraba da tsofaffin ‘ya ‘yan na NNPP da PDP, ya nuna za a rika damawa da su a jam'iyyar APC.

Shugaban na APC ya ce wata kungiya mai suna Kwankwasiyya ce ta gurbata jam’iyyar NNPP mai alamar kayan dadi, ta yi mata kaka-gida.

"Dole ayi mana wanka a APC"

Shuaibu Abdullahi ya na cikin ‘ya ‘yan NNPP kuma magoya bayan Sulaiman Hunkuyi a Kaduna ta Arewa a takarar Gwamna da aka yi a 2023.

Da mu ke magana da shi, ya shaida mana cewa dolensu ne su bar NNPP mai kayan dadi, su shigo APC mai-ci domin a dama da su a siyasar yau.

APC za ta karbe Kano a hannun NNPP - Ganduje

Abdullahi Ganduje ya ce Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba ta da farin jini, ana da labari ya sha alwashin APC za ta koma kan mulkin jihar Kano.

Shugaban na APC ya ce galabar Ado Doguwa a kotun zabe ya nuna za a tunbuke NNPP a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel