An shiryawa Sanata Suleiman Hunkuyi gagarumar tarbar dawowa Jam’iyyar PDP a Kaduna

An shiryawa Sanata Suleiman Hunkuyi gagarumar tarbar dawowa Jam’iyyar PDP a Kaduna

Mun samu labari cewa Sanatan Kaduna ta Arewa watau Suleiman Othman Hunkuyi da sauran Mabiyan sa za su tattara kayan sa su kaf su fice daga Jam’iyyar APC mai mulki su koma Jam’iyyar PDP.

An shiryawa Sanata Suleiman Hunkuyi gagarumar tarbar dawowa Jam’iyyar PDP a Kaduna

Sanata Suleiman Hunkuyi zai ja da Gwamna El-Rufai

Sanata na Arewacin Jihar Kaduna Suleiman Othman Hunkuyi yayi ban-kwana da Jam’iyyar APC inda zai koma Jam’iyyar da yayi a baya watau PDP. Babban ‘Dan siyasar zai fice daga APC ne da dinbin Mabiya bayan sa a Jihar.

Kamar yadda labari ya zo mana, an shirya tarbar ‘Dan Majalisar Dattawan a filin kasuwar baja-koli da Duniya da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zaria a Ranar Litinin. Magoya bayan ‘Dan siyasar da ke karkashin APC za su koma PDP.

KU KARANTA: Buhari bai da tamka a kaf Kasar nan - Inji wani 'Dan fim

Bayan kafa Gwamnatin APC a Jihar Kaduna ne Sanata Suleiman Hunkuyi ya samu matsala da Gwamna Nasir El-Rufai. Yanzu haka ‘Yan tawaren Jam’iyyar APC da ke R-APC duk za su bi Sanatan Jihar zuwa Jam’iyyar adawa.

Ana tunani cewa Suleiman Hunkuyi zai nemi takarar Gwamna ya kara da Gwamna mai-ci Nasir El-Rufai a zabe mai zuwa. A shekarun baya Hunkuyi yayi takarar Gwamnan na Jihar Kaduna amma bai taba nasarar kai labari ba.

Shekaran jiya kuma jun ji cewa rikicin da ke tsakanin Sanatan Kaduna Shehu Sani da kuma Gwamnan Jihar Mai girma Malam Nasir El-Rufai ya kara kunno kai inda har ta kai Jam’iyya na ta haka ne-ba haka ba game da dakatar da shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel