Jigon LP Ya Bayyana Gaskiyar Abinda Ke Cikin Takardun Peter Obi

Jigon LP Ya Bayyana Gaskiyar Abinda Ke Cikin Takardun Peter Obi

  • Peter Obi ya shiga layi yayin da jigon LP ya fallasa ruɗanin da ke tattare da takardun karatunsa
  • Mai magana da yawun LP na ƙasa a tsagin Apapa ya ce sunan Obi ya sha banban a takardar digiri da kuma ta NYSC
  • Abayomi Arabambi ya ce yana ɗaya daga cikin waɗanda suka tantance Obi yayin zaɓen fidda ɗan takarar Labour Party

FCT Abuja - Sakataren watsa labarai na jam'iyyar LP ta tsagin da Lamidi Apapa ke jagoranta, Abayomi Arabambi, ya fallasa kashin da ke tattare da takardun karatun Peter Obi.

Jigon Labour Party ya yi zarcin cewa akwai ruɗani a takardun ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar watau Peter Obi, inda ya ce yana cikin waɗan da suka tantance shi.

Peter Obi.
Jigon LP Ya Bayyana Gaskiyar Abinda Ke Cikin Takardun Peter Obi Hoto: Mr Peter Obi
Asali: Twitter

Mista Arabambi, ya yi wannan furucin ne a wata hira da AIT yayin da yake martani kan kalaman da Obi ya yi game da shaidar karatun Bola Tinubu ta jami'ar Chicago.

Kara karanta wannan

Ombugadu Na PDP Ya Yi Martani Kan Batun Cewa Zai Tube Rawanin Sarakuna Da Zarar Ya Hau Mulki a Nasarawa

Kakakin LP na kasa ya ce yana cikin mutanen da suka tantance Obi kafin zaben fidda gwani na ɗan takarar shugaban kasa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ruɗanin da ke cikin takardun Peter Obi

A cewarsa, sunan da aka rubuta a kan takardar shaidar karatu ta Obi daga Jami’ar Najeriya, Nsukka (UNN), ba iri ɗaya bane da wanda aka rubuta a takardar shaidar bautar kasa NYSC.

"Mu muka tantance shi, a Fam EC9 da muka ba shi, ya cike cewa jami'ar UNN ta ba shi shaidar digiri kuma ya yi aikin bautar ƙasa amma abin takaicin, sa'ilin da ya dawo da Fam ɗin, takardar makaranta kadai ya kawo."
"Saboda haka akwai wani ɓoyayyen al'amari, kuma ina mai faɗa muku cewa sunansa da makaranta ta tura ya sha banban da sunan da ke jikin Satifiket ɗinsa na NYSC."

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai Ta Ƙasa Ta Ɗage Zamanta Yayin da Ɗan Majalisar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

"Bamu san ina ya dosa ba, ga ƙara ya kai gaban Kotun koli kuma bai yi bayani kan wannan ba, amma yana da bakin da zai kira wani ya fito ya faɗi hakiƙanin bayanansa."
"Ko mu bamu san haƙikanin waye Peter Obi ba, ko a jam'iyyar LP saboda komai an yi shi ne a lulluɓe tsakaninsa da Abure a Asaba," in ji shi.

Kashim Shettima da Gwamnonin APC Sama da 10 Sun Dira Jihar Imo

A wani rahoton kuma Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya isa jihar Imo domin halartar gangamin yaƙin neman zaɓen APC.

Gwamna Hope Uzodinma da wasu gwamnonin APC ne suka je filin.sauka da tashin jiragen sama suka tarbi Shettima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262