Rikicin NNPP: Tsohon Shugaban Jam'iyya Na Kasa, Rufa'i Ya Fice Daga NNPP
- Tsohon shugaban jam'iyyar NNPP na kasa, Farfesa Rufai Ahmed Alkali, ya fice daga jam'iyyar bayan rigingimun da suka ɓarke
- A wata sanarwa ranar Talata, Rufai ya bayyana cewa ya fahimci wannan rikicin da ya raba NNPP gida biyu ba mai ƙarewa bane
- Ya ce a baya ya sauka daga muƙamin shugaban NNPP na kasa ne domin ba wasu dama su gwada ta su basirar amma abu ya lalace a yanzu
FCT Abuja - Farfesa Rufa'i Ahmed Alkali, tsohon shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), ya fice daga jam'iyyar, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a birnin tarayya Abuja, Rufa'i ya bayyana cewa ya yanke hukuncin barin NNPP ne, "Bayan faɗaɗa neman shawari."
Masu sharhi kan harkokun siyasa na kallon matakin na Rufa'i a matsayin babban koma baya ga jam'iyyar wacce ke fama da babban rikicin da ya raba kawunan mambobinta.
Tsohon shugaban NNPP na ƙasa, Rufa'i ya yi murabus daga muƙaminsa a ranar 31 ga watan Maris, inda ya ce ya sauka ne domin bai wa wasu dama.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rikicin NNPP ba mai ƙarewa bane - Rufai
A kalamansa, Farfesa Rufa'i ya ce:
“Lokacin da na yi murabus daga matsayin shugaban jam'iyya, na so NNPP ta haɓaka tare da karfafa wuraran da ta samu nasara a babban zaben 2023 da kuma shirya tunkarar zabe na gaba."
“Abin takaici, a cikin ‘yan makonnin da suka gabata, jam’iyyar ta tsunduma cikin rikice-rikicen da za a iya kaucewa, wadanda suka kai ga dakatar da wasu jiga-jigai."
"Abubuwna sun dagule a cikin jam'iyya, mambobi na yaƙar junansu a fili, wadan nan su soki waɗan can, su kuma su rama, abin takaicin har ta kai ga jam'iyyar ta dare gida biyu."
Gaskiya Ta Fito: Obasanjo Ya Bayyana Abinda Ya Sa Ya Ɗauko Umaru 'Yar'adua Duk Ya San Ba Shi Da Lafiya
“Hakika wannan abin takaici ne kuma tasgaro ne mai girma ga ci gaban kowace jam’iyyar siyasa, musamman jam'iyya mai tasowa kamar NNPP."
Daga ƙarshe, Rufa'i ya bayyana cewa bayan tattaunawar neman shawari da makusanta, ya yanke shawarin fice wa daga jam'iyyar baki ɗaya, Vanguard ta tattaro.
Malam Saidu Abdu, jigon jam'iyyar NNPP a jihar Kano ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa suna fatan shawo kan duk wani saɓani da ya shiga tsakanin shugabanni a matakin ƙasa.
A cewarsa, batun dakatar da ɗan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ba abu ne mai yuwuwa ba, domin ta dalilinsa ne jam'iyyar ta shiga lungu da saƙo a Najeriya.
Malam Saidu ya ce:
"Abun takaici ne yadda muka tsinci kanmu a NNPP, idan har ana son kawo ci gaba to dole shugabannin da suke faɗa da juna a matakin ƙasa su sulhunta kansu."
"Ba zai yuwu a dakatar ko a kori Kwankwaso ba, to waya jagoranci NNPP har mutane suka san ta? Ai saboda yana takara ne yan Najeriya a ko ina suka san jam'iyyar."
NNPP Ta Kori Rabiu Kwankwaso Daga Jam’iyyar
Kuna da labarin Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta kori da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Kwankwaso.
Hakan ya biyo bayan dakatar da shi da shugabancin NNPP ya yi a lokacin babban taron jam’iyyar na kasa wanda aka yi a Lagas a karshen makon watan Agusta.
Asali: Legit.ng