Asari Dokubo Ya Kai Wa Shugaban APC Abdullahi Ganduje Ziyarar Taya Murna a Abuja
- Fitaccen ɗan rajin kare haƙƙin yankin Neja-Delta, Asari Dokubo, ya kai wa Abdullahi Ganduje ziyara
- Dokubo ya kai wa tsohon gwamnan jihar Kano wannan ziyara ne a gidansa da ke Abuja a ranar Lahadin da ta gabata
- Ya je ne domin ya taya Ganduje murnar nasarar zaman shugaban jam'iyyar APC da ya yi a ranar 3 ga watan Agusta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Fitaccen ɗan rajin kare haƙƙin yankin Neja-Delta, Alhaji Mujahid Asari Dokubo, ya kai wa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ziyara.
Dokubo ya ziyarci Ganduje ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta a gidansa da ke Abuja kamar yadda aka wallafa a shafin jam'iyyar wato @OfficialAPCNg na X.
Asari Dokubo ya je taya Ganduje murnar zama shugaban APC
Hadimin Atiku Ya Fadi Iya Wa'adin Da Ya Ragewa Bola Tinubu a Kan Kujerar Shugabanci, Ya Ba Shi Shawara
An bayyana cewa Asari Dokubo ya ziyarci Ganduje a gidansa da ke Abuja domin taya shi murnar zama sabon shugaban jam'iyyar APC da ya yi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An dai zabi Ganduje a matsayin shugaba da kuma Ajibola Basiru matsayin sakataren jam'iyyar APC na ƙasa makonni uku da suka gabata.
Zaben na Ganduje da Basiru ya biyo bayan saukar tsohon shugaba da sakataren APC, Abdullahi Adamu da kuma Oyiola Omisore bi da bi.
Ganduje ya sha alwashin warware rikicin da ya kunno kai a APC
A baya Legit.ng ta yi rahoto kan rikicin cikin gida na jam'iyyar APC da shugabanta Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin warwarewa.
Saɓani ya dai kunno kai ne a cikin jam'iyyar mai mulki jim kaɗan bayan bayyanar sunayen sabbin mambobin kwamitin gudanarwa da jam'iyyar ta zaɓa.
Ganduje bayan ganawa da ya yi da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya bayyana cewa zai warware rikicin jam'iyyar cikin ruwan sanyi.
'Yan sanda sun mamaye babbar sakatariyar APC ta ƙasa
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan mamayar da jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya suka yi wa babbar sakatariyar jam'iyyar APC mai mulki ta ƙasa.
Hakan dai ya faru ne a daidai lokacin da jam'iyyar ta APC ke shirin sanar da sabbin mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) na ƙasa na da ta zaɓa.
Asali: Legit.ng