Dalilin Da Yasa Ba a Taba Jin Kaina Da Bagudu Ba, Tsohon Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Magantu

Dalilin Da Yasa Ba a Taba Jin Kaina Da Bagudu Ba, Tsohon Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Magantu

  • Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Kanal Ismaila Yombe ya bayyana sirrin zaman lafiyar da suka yi da Atiku Bagudu a mulki
  • Yombe wanda ya kasance tsohon soja ya ce yana bin duk wani umurni da tsohon gwamnan na jihar Kebbi ya ba shi ba tare da jayayya ba
  • A cewarsa, yana kokarin ganin bai keta iyakar da kundin tsarin mulki ya tanadar masa ba a matsayinsa na mataimaki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kebbi - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Kanal Ismaila Yombe mai ritaya, ya bayyana cewa ya mutunta hakkin da kundin tsarin mulki ya ba tsohon ubangidansa, tsohon gwamna Atiku Bagudu.

A cewar Yombe, wannan ne dalilin da ya sa ba su taba shiga wani rikicin siyasa da Bagudu ba a lokacin da suke yi wa jihar hidima, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kujerar Minista: Uba Sani Ya Magantu Kan Zargin Yi Wa El-Rufai Tuggu a Wurin Tinubu

Yombe ya ce ba a taba jin bakinsu da Bagudu ba saboda bai keta iyakarsa ba
Dalilin Da Yasa Ba a Taba Jin Kaina Da Bagudu Ba, Tsohon Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Magantu Hoto: @atikuabagudu
Asali: Twitter

Na bi Bagudu sau da kafa shiyasa ba a ji kanmu ba, Yombe

Tsohon mataimakin gwamnan na Kebbi ya ce ya yi amfani da horon da ya samu a aikin soji sannan ya dungi bin umurnin Bagudu wanda a karshe ya ci riba a cikin gwamnatinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yombe ya bayyana hakan ne a cikin wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Daily Trust a shirin siyasar kullun.

Ya ce:

"Hakkin gwamnan a kundin tsarin mulki shine ya jagorance ni. Zai ba da umarni a kan abun da zan yi kuma zan yi shi cike da karfin gwiwa.
“Hakan ya taimaka mun wajen ci gaba da kasance a iya wajen da kundin tsarin mulki ya tanadar mun. Kuma shakka babu, na yi amfani da horon da na samu a matsayin soja, ina jure duk wani abu da zai haifar da rashin fahimta.

Kara karanta wannan

WAIWAYE: ‘Na Fi So Na Ba Tinubu Gudunmawa Daga Waje’, El-Rufai Ya Magantu Kan Mukamin Minista

“Saboda haka ba mu samu wata matsala ba ko kadan a tsawon aikinmu a matsayin gwamna da mataimakin gwamnan jihar Kebbi.”

Na kusa yanke kauna, tsohon gwamnan Kebbi

Tsohon kanal din ya kara da cewar akwai wasu lokuta marasa dadi a lokacin da yake kujerar mulki, amma ya yanke shawarar ci gaba da zama bayan nazarin halin da ake ciki.

"Eh akwai lokacin da na kusa yin haka (lokacin da na kusa hakura) amma na ki bayan na yi nazarin halin da ake ciki.
“A lokacin ne na yanke shawarar tallafa wa mutanen da ke yaki (sojoji) da wani nau’in sufuri da zai samar da ingantaccen tsaro fiye da yadda suke da su a yanzu. Nan take abun ya yi tasiri."

Malamin addini ya gargadi yan majalisar Najeriya

A wani labari na daban, Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya ce ya hango ana yi wa yan majalisar wakilai da sanatoci jifa da duwatsu dare da ihun ba ma yi.

Saboda haka, malamin addinin ya shawarci yan majalisa da su zamo masu lura da addu'a domin dakile "wannan mummunan al'amari".

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: