Tinubu Ya Ce Ya Yi Nasarar Lashe Zaɓe Salin Alin Duk Da Tarkon Da Aka Dana Ma Sa

Tinubu Ya Ce Ya Yi Nasarar Lashe Zaɓe Salin Alin Duk Da Tarkon Da Aka Dana Ma Sa

  • Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya bayyana abubuwan da suka wakana a lokacin zaɓen 2023
  • Tinubu wanda ya lashe zaɓen, ya bayyana yadda wasu suƙa ƙulla masa makirci domin ganin bai yi nasara ba
  • Sai dai ya ce ya lashe zaɓen ba tare da wani tsaiko ba duk da tuggun da aka shirya masa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi mai muhimmanci dangane da nasarar da ya samu a zaɓen 2023 da ya gabata.

Tinubu a muhimmin jawabinsa yayin taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) na jam'iyyar APC karo na 12 a ranar Alhamis, ya bayyana cewa yana sane da cewa wasu mutane sun ɗana ma sa tarko gabanin zaɓen 2023.

Tinubu ya ce an kulla ma sa makirce-makirce gabanin zabe
Tinubu ya ce yana sane da mutanen da suka shirya ma sa makarkashiya gabanin zabe. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Na lashe zaɓe na salin alin, Tinubu ya faɗa a wajen taron NEC

Kara karanta wannan

Tinubu: Adadin Ministocin Da Shugabannin Najeriya Suka Naɗa Daga 1999 Zuwa Yau

Tinubu ya ce duk da yana sane da mutanen, sai ya biye musu domin ya nuna musu cewa zai iya lashe zaɓen duk da ƙulle-ƙullen na su kamar yadda The Punch ta wallafa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake magana kan shari'ar zaɓe da ke gaban kotu, Tinubu ya ce masu jayayya da nasarar ta sa ba su cancanci jin daɗin nasara ba.

Ya ce zaɓen 2023 da ya gabata, yana daga cikin sahihan zaɓukan da aka taɓa gudanarwa a tarihin Najeriya kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Tinubu ya ƙara da cewa, sun yi aiki tuƙuru wajen ganin sun yi nasara a zaɓen na 2023 da ya gabata, wanda kuma ga shi yanzu haka kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

An zabi Ganduje da Basiru matsayin jagororin APC

A yayin babban taron na jam'iyyar APC wanda a nan ne Tinubu ya yi waɗannan jawabai, an zaɓi tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

"Yan Najeriya Suna Farin Ciki da Mulkinka" An Faɗa Wa Shugaba Tinubu Halin da Mutane Ke Ciki

Haka nan an zaɓi tsohon mai magana da yawun Majalisar Dattawa ta tara, Ajibola Basiru a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa.

Da yake jawabi bayan amsar naɗin da aka yi masa, Abdullahi Ganduje ya yi alƙawarin haɗa kawunan duka 'ya'yan jam'iyyar ta APC.

Ganduje ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su ƙara haƙuri da gwamnatin Tinubu, inda ya ce za a ji daɗin tsare-tsaren da shugaban ya zo da su a nan gaba.

Buhari ya bayyana abinda ya sa bai halarci babban taron APC ba

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da ya bayyana dalilin da ya sai bai samu damar halartar babban taron jam'iyyar APC na ƙasa ba.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce wasu alƙawura da ya yi ne suka hana shi halartar taron na APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng