Tawfiq Akinwale, Dan Takarar Gwamnan Jam'iyyar Labour a Oyo Ya Koma APC

Tawfiq Akinwale, Dan Takarar Gwamnan Jam'iyyar Labour a Oyo Ya Koma APC

  • Dan takarar gwamnan jihar Oyo a jam'iyyar adawa ta Labour Tawfiq Akinwale, ya fice daga jam'iyyar zuwa APC
  • A cewar Akinwale, ya dauki wannan matakin ne saboda irin burirrikan da yake da su na gani jihar ta Oyo ta ci gaba
  • Ya ce jam'iyyar adawa ta Labour ba ta da wasu tsaruka masu kyau na ci gaban jihar da ma kasa baki daya

Oyo - Dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar Labour a jihar Oyo Tawfiq Akinwale, ya fice daga jam'iyyar inda ya koma jam'iyyar APC mai mulki.

A wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Lahadi, Tawfiq ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa APC ne bayan nazari da ya yi kan yadda harkokin siyasa ke tafiya.

Dan takarar gwamna a jihar Oyo ya fice jam'iyyar Labour zuwa APC
Dan takarar gwamnan jam'iyyar Labour a jihar Oyo ya koma APC saboda rashin manufa. Hoto: @LabourParty_Oyo
Asali: Twitter

Jam'iyyar Labour ba ta da tsaruka masu amfani ga kasa

Kara karanta wannan

“Aikin Nan Akwai Hatsari Sosai”: Mai POS Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Karbi Jabun N100K Daga Kwastoma, Bidiyon Ya Yadu

Ya ce a iya nazarin da ya gudanar, ya fahimci cewa tsohuwar jam'yyarsa ta Labour ba ta da wasu tsare-tsare na samar da ci gaban da ake bukata a jihar da ma kasa baki daya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kara da cewa jam'iyyar ta Labour a jihar ta rasa inda ta sa gaba, sabanin APC da take da kudurori da za su matsar da jihar ta Oyo zuwa gaba kamar yadda Vanguard ta wallafa.

a kalamansa:

"A lokacin yakin neman zabe, na fahimci irin yadda mutanen jihar Oyo suka zaku wajen samun canji na gari da kuma samun ci gaba. Na lura da cewa ba za a samu irin wannan canji ba a karkashin shugabancin jam'iyyar ta Labour a jihar."
"Don haka, bayan na yi nazari sosai, na yanke shawarar shiga jam’iyyar APC, jam’iyyar da ke da muradin ci gaba, hadin kai, da jagoranci mai ma’ana.”

Kara karanta wannan

Labari Ya Canja: Yan Sanda Sun Binciko Gaskiyar Yadda Wata Budurwa Ta Mutu a 'Hotel'

APC na son gina 'yan Najeriya

Tawfiq ya kuma bayyana cewa, jam'iyyar APC ta tabbatarwa da 'yan Najeriya irin kudirorinta na san samar da kyakkyawan shugabanci, daga tattalin arziki da kuma gina 'yan kasa.

Ya ce duk da halin matsi da aka shiga a halin da ake ciki, 'yan Najeriya za su yi dariya nan ba da jimawa ba.

Ya kara da cewa yana da tabbacin cewa jam'iyyar ta APCa jihar Oyo, za ta ba shi dama ta musamman ya hadu da mutane irinsa masu son ci gaban jihar, wajen kawo tsarukan da za su cika burinka al'umma.

Ya kuma ce babban dalilin komawarsa jam'iyyar APC mai mulki, shi ne saboda ci gaban da yake burin ganin an samu a jihar Oyo da Najeriya baki daya.

Jam'iyyar Labour yi wa 'yan Najeriya shagube kan cire tallafin man fetur

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan shaguben da jam'iyyar Labour ta yi wa 'yan Najeriya duba da halin da suke ciki na radadin cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Anya Ganduje Zai Kai Labari? Gaskiya Ta Bayyana Kan Wanda Zai Zama Sabon Shugaban APC

Jam'iyyar ta ce halin da 'yan Najeriya ke ciki a yanzu ba komai ba ne kan abinda zai biyo baya a gwamnatin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng