Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Ajiye Zababben Kwamishina Da EFCC Ta Gurfanar

Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Ajiye Zababben Kwamishina Da EFCC Ta Gurfanar

  • Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya soke sunan Dr. Ibrahim Yusuf Ngoshe daga cikin jerin kwamishinoninsa
  • A ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli ne Zulum ya aika sunayen mutane 18 zuwa majalisar dokokin jihar Borno don tabbatar da su
  • Sai dai da yake fitar da sanarwar, kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau bai bayyana dalilin cire sunan Ngoshe da aka yi ba

Jihar Borno - Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya cire sunan Dr. Ibrahim Yusuf Ngoshe daga cikin jerin wadanda ya ke son nadawa a matsayin kwamishinoninsa.

A wata wasika da ya aike zuwa majalisar dokokin jihar Borno a yammacin ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli, Gwamna Zulum ya bukaci yan majalisa da su cire sunan Yusuf Ngoshe daga cikin jerin kwamishinonin da ya aike masu.

Kara karanta wannan

Tausayin talaka: Zulum da wasu gwamnoni 2 sun kawo hanyar rage radadin cire tallafi

Gwamnan Borno ya soke sunan daya daga cikin kwamishinonin da ya mika majalisa
Yanzu Yanzu: Gwamnan Borno Ya Cire Sunan Yusuf Ngoshe Cikin Wadanda Za a Nada Kwamishinoni Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

Kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, 29 ga watan Yuli, ya yi bayanin cewa da wannan, adadin kwamishinonin da aka zaba ya ragu daga 18 zuwa 17.

Sai dai kuma, Malam Gusau bai bayyana ainahin dalilin cire sunan Ngoshe ba amma ya ce za a gabatar da karin bayani kan lamarin idan bukatar hakan ya taso.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli ne Gwamna Zulum ya aike sunayen mutane 18 majalisar dokokin jihar domin tantancesu da kuma tabbatar da su a matsayin kwamishinoninsa.

EFCC na shari'a da Ngoshe

Ngoshe wanda ya kasance haifafen yankin Borno ta kudu a karamar hukumar Gwoza yana cikin yan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da suka nemi tikitin takarar kujerar dan majalisar jiha mai wakiltan Gwoza amma ya sha kaye.

Kara karanta wannan

Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Gagarumin Hasashe Game Da Ministocin Shugaban Kasa Tinubu

Sai dai ba a tabbatar da ko shari'ar da ahukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC ke yi da Ngoshe bane ya tunzura gwamnan zuwa daukar wannan mataki na cire shi daga cikin kwamishinoninsa.

A watan Maris, hukumar EFCC reshen Maiduguri ta gurfanar da Ngoshe a gaban Justis Aisha Kumaliya ta babbar kotun jihar Borno kan tuhumarsa da ake yi na wawure kudi N24,000,000.00.

Ya ki amsa tuhumar da ake masa, yayin da alkaliyar ta tsare shi sannan ta dage shari'ar har zuwa watan Mayu, Daily Trust ta rahoto.

Gwamna Zulum ya rantsar da manyan jami'an gwamnatinsa

A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya rantsar da shugaban ma'aikatan jihar da wasu mutum biyu masu ba shi shawara na musamman.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa gwamnan ya kuma rantsar da shugabannin riƙon ƙwarya na ƙananan hukumomi 27 a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng