Yanzu Yanzu: Mataimakin Shugaban APC Na Kasa Da Ke Adawa Da Ganduje Ya Yi Murabus

Yanzu Yanzu: Mataimakin Shugaban APC Na Kasa Da Ke Adawa Da Ganduje Ya Yi Murabus

  • Rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar APC mai mulki ya dauki sabon salo a ranar Laraba, 26 ga watan Yuli
  • Mataimakin shugaban APC na Arewa maso yamma, Salihu Lukman ya yi murabus daga kan kujerarsa
  • Lukman dai yana adawa da yunkurin da ake yi na maye gurbin Abdullahi Adamu, tsohon shugaban jam'iyyar da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Mataimakin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a Arewa maso yamma, Salihu Mohammed Lukman, ya yi murabus daga kujerarsa, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Mataimakin shugaban APC na kasa ya yi murabus
Yanzu Yanzu: Mataimakin Shugaban APC Na Kasa Da Ke Adawa Da Ganduje Ya Yi Murabus Hoto: Comrade Salihu Lukman, Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Dalilin da yasa Lukman ya yi murabus

Lukman, wanda ya kasance mamba a kwamitin aiki na APC, ya bayyana cewa ya yi murabus ne saboda yanayin abubuwa a jam'iyyar mai mulki wanda ya saba da manufar kafa jam’iyyar.

Kara karanta wannan

"Tsohon Shugaban Majalisa Ya Jawowa Abdullahi Adamu Rasa Shugabacin APC"

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai kwanan watan 26 ga watan Yuli, kuma ya aika wa mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abubakar Kyari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce zai zama kisan kai da kai maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu, tsohon shugaban jam'iyyar mai mulki na kasa da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje.

Lukman yana adawa da shirin baiwa Ganduje shugabancin APC

Tun farko dai mun ji cewa Salihu Lukman ya rubuta takarda zuwa ga gwamnonin da ke mulki a jam’iyya mai-mulki.

Vanguard ta rahoto cewa Lukman ya aika wasika zuwa ga Gwamnan jihar Imo, yana gargadi kan yin adalci game da wanda zai zama shugaban APC, inda ya ce ya kamata gwamnoni su zama tamkar kwakwalwar jam'iyyar mai mulki a halin da ake ciki.

Kafin gwamnonin su cin ma matsaya, mataimakin shugaban na APC ya ce ya kamata a fara zama da NWC a game da wanda zai jagorance su.

Kara karanta wannan

Abdullahi Ganduje Ya Huro Wuta Wajen Ganin Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC

Primate Ayodele ya ce Al-Makura ne ya cancanci zama shugaban APC ba Ganduje ba

A baya mun kawo cewa, Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ya bayyana Tanko Al-Makura, tsohon gwamnan jihar Nasarawa a matsayin wanda ya fi cancanta da zama shugaban APC na kasa.

Malamin addinin ya kuma yi hasashen cewa baiwa Abdullahi Umar Ganduje ko wani daban shugabancin jam'iyyar mai mulki zai kara jefa ta cikin sabon rudani ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng