Gwamnatin Jigawa Ta Nemi a Karbo Ma Ta Kadarorinta Wurin Gwamnatin Kano
- Gwamnatin jihar Jigawa ta nemi a kwato ma ta wasu muhimman kadarorinta daga hannun gwamnatin Kano
- Gwamnatin ta Jigawa ta yi ikirarin cewa akwai kadarorinta da aka rike ma ta su tun bayan raba jihar Kano da Jigawa
- Ta nemi hukumar Yaki da Rashawa da Karbar Korafe-Korafe (PCACC), da ta taimaka ma ta wajen samun kadarorin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa, ta nemi a kwato ma ta wasu kadarorinta da ta ce gwamnatin Kano ta cinye.
Gwamnatin ta Jigawa ta nemi Hukumar Yaki da Rashawa da Karbar Korafe-Korafe (PCACC), da ta taimaka ma ta wajen karbor hakkinta da ta ce an cinye.
Kwamishinan ayyuka na musamman na Jihar Jigawa, Auwal Sankara ne ya yi wannan kira ga babban sakataren hukumar, Muhuyi Magaji Rimingado kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kadarorin da gwamnatin jihar Jigawa ke neman a kwato ma ta
Sankara ya bayyana cewa kadarorin da suke magana an ware su ne a shekarar 1993, wato bayan raba jihar Kano da Jigawa a matsayin kasonta a wancan lokaci.
Ya kara da cewa a ranar 5 ga watan Mayun shekarar 1993 ne aka gabatar da shedar da rabon, wacce gwamnan Kano na lokacin Kabir Ibrahim Gaya, da na Jigawa Ali Sa'ad Birnin Kudu suka sanyawa hannu.
Daga cikin kadarorin a cewar Sankara akwai wani filoti mai lamba 133 da ke kasuwar Farm Center da aka mallakawa Jigawa a lokacin.
Haka nan ya kara da cewa akwai wasu kadarorin da ke a titin Maiduguri, Sharada da Sulaiman Crescent kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.
Ya kuma bayyana cewa tun bayan kirkirar jihar Jigawa daga Kano suke ta faman ganin sun karbi wadannan kadarorin, amma kuma abin ya ci tura.
Muhuyi Magaji ya ce suna kan gudanar da bincike a kan lamarin
Shugaban hukumar ta PCACC Muhuyi Magaji Rimingado ya bayyana cewa koken ya iso gare shi.
Muhuyi ya kuma bayyana cewa a yanzu haka ma har sun fara gudanar da bincike a kan lamarin.
Ya kara da cewa suna kokarin gano inda kadarorin suke, wanda daga nan ne za su ga yadda za a yi wajen mayarwa masu koken hakkinsu.
Dan wasan kwallon super Eagles ya karya farashin litar man fetur a gidan mansa
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan fitaccen dan wasan kwallon kafar nan na Super Eagles wato Ahmed Musa, ya karya farashin litar man fetur zuwa naira 580 a gidan mansa da ke Kano.
Shahararren dan wasan kwallon ya yi hakan ne domin tausayawa talakawa saboda halin da ake ciki na tsadar man fetur.
Asali: Legit.ng