Al-Makura Ne Ya Cancanci Zama Shugaban APC Na Kasa, Primate Ayodele
- Primate Elijah Ayodele ya ba da shawarar cewa Sanata Tanko Al-Makura, tsoho gwamnan jihar Nasarawa ne ya kamata a nada a matsayin shugaban APC na kasa
- Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ya yi gargadin cewa zabar wani dan takara kamar Abdullahi Umar Ganduje, zai kara zurfafa rikcin jam'iyyar
- Ayodele ya yi ikirarin cewa an yi watsi da shawarar da ya bayar a baya na zanar Al-Makura, wanda ya haifar da matsalolin da aka fuskanta a lokacin mulkin Abdullahi Adamu
Jihar Lagos - Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ya ce mutumin da ya fi dacewa da shugabancin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) shine tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura.
Malamin addinin wanda ya yi suna wajen yin hasashe ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinsa, Osho Oluwatosin.
Dalilin da yasa ya kamata ku zabi Almakura, Ayodele ga APC
Primate Ayodele ya shawarci jam'iyya mai mulki da ta zabi Al-Makura a matsayin shugabanta na gaba saboda shi kadai ne wanda shugabancinsa ba zai jefa jam'iyyar cikin rikici ba, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Malamin addinin ya kara da cewar a baya ya shawarci APC da ta zabi Al-Makura kafin jam'iyyar mai mulki ta zabi Abdullagi Adamu wanda ya yi murabus a kwanan nan.
"Mutumin da ya fi dacewa da zama shugaban jam'iyyar All Progressive Congress(APC) na kasa shine Sanata Tanko Al-Makura," in ji shi.
Ya yi ikirarin cewa rashin jin gargadinsa da APC bata yi ba shine ya haddasa rikicin da ya yi sanadiyar murabus din Adamu.
Legit.ng ta lura cewa jawabin Ayodele na zuwa ne bayan rade-rdin cewa shugaban kasa Tinubu ya amince da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin shugaban APC na gaba.
Abun da zai faru idan Ganduje ya zama shugaban APC, Ayodele
Da yake ci gaba da jawabi, Primate Ayodele ya ce jam'iyyar mai mulki za ta kara zurfafa a cikin rikici idan ta zabi Ganduje, tsohon gwamnan Kano a matsayin shugabanta na gaba.
“Idan Ganduje ko wani mutum ya samu wannan mukami, jam’iyyar za ta fada cikin rikici fiye da yadda take fuskanta a yanzu.
‘’Idan jam’iyyar na son ci gaba, to su zabe shi a matsayin shugaba na gaba. Na fada musu kafin zabar Adamu cewa Al-Makura ne ya fi cancanta amma ba su ji ba, kuma yanzu sun biya bashi.
''Wannan wata dama ce ta gayara kuskure. Idan suna son su saurara idan kuma ba su yi ba, to matsalarsu ce, amma sakon da nake da shi a garesu, Tanko Al-Makura shi ne wanda ya fi kowa cancanta a zaba.” Inji malamin.
Yan Najeriya sun yi martani a kan yunkurin nada Ganduje a matsayin shugaban APC na kasa
A baya Legit.ng ta rahoto cewa, akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na duba yiwuwar nada tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.
Hakan zai zama cike gurbin da tsohon shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya bari.
Asali: Legit.ng