Ganduje Zai Dawo Da Kwankwaso Da Mukarrabansa Zuwa APC, Musa Iliyasu
- Kwamishina a tsohuwar gwamnatin jihar Kano ya bayyana abin da Abdullahi Ganduje zai fara yi idan ya zama shugaban APC
- Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce Ganduje zai fara ne da karɓar mutane zuwa jam'iyyar ta APC mai mulki a kasa
- Ya ce daga cikin mutanen da Ganduje zai karɓa akwai Kwankwaso da sauran 'yan jam'iyyarsa
Kano - Kwamishinan raya karkara a gwamnatin Kano da ta shuɗe, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa Ganduje zai karɓi Kwankwaso da 'yan jam'iyyarsa zuwa APC da zarar ya zama shugaban jam'iyyar.
Ya bayyana hakan ne a cikin shirin Kowane Gauta na gidan rediyon Freedom Kano a yayin da yake tsokaci kan shugabancin APC da ake hasashen bai wa Ganduje.
Ganduje ya amince da tayin da aka yi masa
Musa Iliyasu ya bayyana cewa Shugaba Tinubun, Kashim Shettima, shugaban Majalisar Dattawa da wasu gwamnoni ne suka yi wa Ganduje tayin kujerar shugabancin jam'iyyar APC.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Iliyasu ya kuma ce Ganduje ya karɓi tayin shugabancin da aka yi masa ba tare da wata shilafa ba, har ma sun yi masa fatan alkahiri.
Ya ƙara da cewa Ganduje ya yi aiki an gani a Kano, saboda haka jam'iyyar APC za ta haɓaka sa zarar an naɗa shi a matsayin sabon shugaban jam'iyyar.
Musa ya ce za su karɓi Kwankwaso bayan ƙwace kujerar gwamnan Kano
Sannan ya ƙara da cewa da zarar an tabbatar da Ganduje a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC, abu na farko da zai fara yi shi ne karɓar mutane cikin jam'iyyar.
Ya ce za su karɓi Rabiu Kwankwaso zuwa cikin APC da zarar sun karɓi kujerar Abba Gida Gida wacce ɗan takarar gwamna na APC a Kano, Nasiru Gawuna ke ƙalubalanta.
Ya bayyana cewa dama sun san cewa Kwankwaso na yi wa Tinubun aiki ne ta ƙarƙashin ƙasa.
Ya godewa Tinubu bisa muƙamin da ake shirin bai wa Ganduje
Musa Iliyasu ya kuma godewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan muƙamin shugabancin jam'iyyar ta APC da ya nuna yana son a bai wa Ganduje.
Ya ce Ganduje da mutanensa sun bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu gudummawa sosai a can baya.
Musa ya ƙara da cewa, hakan shi ne abinda ya kamata Tinubun ya yi domin mayar da bikin da Ganduje ya yi masa a can baya.
Jigon APC ya bayyana abinda zai faru da APC in aka bai wa Ganduje shugabancin jam'iyyar
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton wani jigon APC da ya nuna rashin amincewarsa kan bai wa Tinubu shugabancin jam'iyyar.
Salihu Lukman, mataimakin shugaban APC na shiyayyar Arewa maso Yamma, ya ce bai wa Tinubu shugabancin zai iya wargaza tsarin jam'iyyar.
Asali: Legit.ng