Hukumar Zabe INEC Ta Amince da Kafa Sabuwar Jam'iyyar Siyasa a Najeriya
- Hukumar zaɓe INEC ta amince da sabuwar jam'iyyar YP da aka kafa a matsayin jam'iyyar siyasa ta 19 a Najeriya
- Kwamishinan INEC na ƙasa, Festus Okoye, ya ce hukumar ta yi wa Youth Party rijista bayan hukuncin kotun ƙoli
- Ya ce daga yanzu jam'iyyar na da dama da alfarmar da za a ba kowace jam'iyya a ƙasar nan
FCT Abuja - Hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta amince da kafa sabuwar jam'iyyar siyasa a Najeriya kuma ta mata rijista.
Rahoton jaridar Daily Trust ya tattaro cewa INEC ta yi wa jam'iyyar Youth Party (YP) rijista a matsayin sabuwar jam'iyyar siyasa a Najeriya.
Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa kuri'a, Festus Okoye, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Alhamis.
Wannan ya nuna cewa a yanzu halastattun jam'iyyun siyasa sun zama 19 kenan bayan samun karin Youth Party (YP) a ƙasar nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dalilin da ya sa INEC ta yi wa jam'iyyar rijista
A sanarwan, kwamishinan INEC ya ce hukumar zaɓe ta yi wa sabuwar jam'iyyar rijista ne sakamakon hukuncin da Kotun kolin Najeriya ta yanke.
A kalamansa, Festur Okoye ya ce:
"Bisa haka, hukumar zaɓe ta amince da Youth Party (YP) a matsayin jam'iyyar siyasa ta 19 a Najeriya kuma daga yanzu tana da dama da duk wata alfarma da kowace jam'iyya ke da shi a ƙasar nan."
INEC ta soke rijistar jam'iyyu 74 gabanin zaɓen 2023
Idan baku manta ba a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2020 hukumar INEC ta soke rijistar jam'iyyun siyasa 74 bisa rashin taɓuka abin a zo a gani a babban zaben 2019.
Shugaban INEC ta ƙasa, Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya bai wa hukumar ƙarfin ikon soke rijistar jam'iyyun siyasa, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Cire Tallafi: Gwamnatin Tinubu Ta Fara Yunkurin Karya Farashin Kayan Abinci
A wani rahoton na daban kuma Gwamnatin shugaba Tinubu ta fara yunkurin sauke farashin kayan abinci a dukkan jihohin ƙasar nan.
NEC ta umarci hukumar NEMA ta raba wa jihohin Najeriya hatsin cikin mako ɗaya ko biyu masu zuwa domin sauko da farashin kayan binci a faɗin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng