Shugaban APC Na Kasa da Sakatare Sun Yi Murabus Ne Bisa Ra'ayin Kansu, Uzodinma
- Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, gwamna Hope Uzodinma na Imo ya yi magana kan abubuwan da ke faruwa a APC
- Uzodinma ya ce Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore sun sauka daga kan muƙamansu ne bisa ra'ayin kansu
- Ya kuma musanta cewa jam'iyyar APC ta shiga cikin sabon rikicin cikin gida, ya ce kan 'ya'yan jam'iyya mai mulki a haɗe yake
FCT Abuja - Ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC ta yi karin haske kan dalilin da ya jawo shugaban jam'iyya, Abdullahi Adamu, da sakatare, Iyiola Omisore suka yi murabus.
Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce jiga-jigan biyu sun yi murabus daga kan muƙamansu ne bisa ganin damarsu, babu wanda ya tilasta musu.
Jaridar Punch ta tattaro cewa gwamna Uzodinma ya faɗi haka ne yayin hira da manema labarai jim kaɗan bayan fitowa daga taron sirri na gwamnonin APC a Abuja.
Taron ya gudana a masaukin gwamnan jihar Imo da ke Asokoro ranar Laraba da daddare kuma rahoto ya nuna cewa sun shiga ganawar da misalin ƙarfe 11:12 na dare.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shin dagaske APC ta faɗa cikin rikici?
Da yake hira da 'yan jarida jim kaɗan bayan kammala taron, gwamna Uzodinma ya musanta raɗe-raɗin cewa jam'iyyar APC na fama da rigingimun cikin gida.
Ya ce gwamnonin jam'iyyar APC na goyon bayan Adamu da Omisore amma bisa ra'ayin kansu suka zabi sauka daga kan muƙamansu.
Jaridar Vanguard ta rahoto Uzodinma na cewa:
"Na san cewa da yawanku kun ƙosa ku san meke wakana a jam'iyyar APC da ƙasa baki ɗaya, mun tattauna batutuwa da dama da suka shafi jam'iyyar mu APC a wannan zaman."
"Na san kuna da labarin murabus din shugaban APC na ƙasa da Sakatare, sun yi haka ne bisa ra'ayin kansu kuma muna girmama su. Mun yaba da hikimar da suka nuna wajen yi wa jam'iyya aiki."
"Mun yaba musu kuma APC a dunƙule take, ba bu wata rigima da ta ɓalle. Sun sauka suna farin ciki kuma mun ji daɗin haka. Don haka muna goyon bayansu kuma ba zamu daina yaba musu ba."
Gwamna Uzodinma ya ƙara da cewa tuni APC ta amince da muraɓus din jiga-jigan biyu kuma ta naɗa shugaba da sakatare na rikon kwarya.
Gwamnatin Benue Ta Bankado Ma'aikatan Bogi 2,500 Daga Fara Bincike
A wani rahoton kuma Gwamnatin jihar Benuwai ta cire ma'aikata 2,500 daga tsarin biyan albashi bayan gano cewa baki ɗayansu na bogi ne.
Gwamna Alia ya ce an gano waɗan nan ma'aikatan ƙaryan ne yayin gudanar da bincike a kan tsarin biyan albashin malamai da ma'aikatan kananan hukumomi.
Asali: Legit.ng