Shugaban APC Na Kasa: Martanin Yan Najeriya Kan Rade-Radin Son Maye Gurbin Adamu Da Ganduje
- Ana ganin Abdullahi Ganduje zai iya maye gurbin tsohon shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu
- Alamu masu karfi sun bayyana cewa an cire sunan Ganduje daga jerin ministocin Shugaban kasa Bola Tinubu
- Yan Najeriya a soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakunansu, wasu na ganin kokari ne na yakice tsohon gwamnan daga ministoci
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na duba yiwuwar nada tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.
Hakan zai zama cike gurbin da tsohon shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya bari kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.
Tuni aka fara rade-radin cewa shugaban kasar ya sauke sunan Ganduje daga jerin ministocinsa wadanda yake shirin bayyanawa.
Hakan na zuwa ne kimanin awanni 48 bayan sanata Abubakar Kyari da Festus Fuanter sun kama aiki a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa da mukaddashin sakataren jam'iyyar mai mulki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da samun wannan labari, yan Najeriya da dama sun garzaya dandalin soshiyal midiya domin bayyana ra'ayoyinsu a kan wannan yunkuri da ake yi.
Yayin da wasu suka goyi bayan haka, wasu na gani ba shi shugabancin jam'iyyar daidai yake da mutuwarta domin a cewarsu zai kasheta murus.
Martanin yan Najeriya kan maye gurbin Adamu da Ganduje
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da mabiyanta na Facebook suka yi a kan wannan yunkuri na mayar da Ganduje shugaban APC na kasa.
Karanta wasu daga cikin martanin a kasa:
Aleeyou Muhammad ya yi martani:
"Allah ko yaushi shine gatanka ganduje uban abba kabuwaye maza."
Mubaraq Sa'eed Kiakia ya ce:
"Shifa Abdullahi Umar Ganduje kowani position yana bugawa har gola yana kamawa."
Jamal Mt Danmaliki ya yi martani:
"Da shugabancin jam'iyya kenan za ayi masa dannar kirji."
Mu'azu Ibrahim Uba Giwa ya ce:
"Abashi babu damuwa, kuma In Shaa Allah, ƙarshen jam'iyyar yazo kenan."
Tanimu Sani Tsakatsa ya ce:
"Waishi dole sai anbashi mukami awannan gwamnatin."
Rufa'i Gambo Isah ya rubuta:
"Gara da aka bashi Jam'iyyar ya karasa kasheta."
Yakubu Muhammad ya ce:
"Ai dama ba jam'iyar arziki bane zata mutu murus wallahi."
Adamu Mubashir ya ce:
"Alamun rushewan apc ya soma ke nan."
Abdul Rasheed Ata ya ce:
"Tab ai shikenan jam'iyar takarasa mutuwa murus kuwa."
Tukur Sama'ila Tsk Kaya:
"Indai akayi hakan Akwai matsala gaskiya."
Tinubu ya bai wa Abdullahi Abbas mukami
A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi majalisar dattawa ta tabbatar da nadin mambobi da shugaban majalisar hukumar bunkasa ci gaban arewa masu gabas (NEDC).
An tattaro cewa Tinubu ya nada shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, a matsayin wakili a majalisar daraktocin hukumar ta NEDC.
Asali: Legit.ng