Shugaban APC Na Kasa Adamu Abdullahi Ya Yi Murabus Ne? Ga Abin Da Muka Sani

Shugaban APC Na Kasa Adamu Abdullahi Ya Yi Murabus Ne? Ga Abin Da Muka Sani

Wani rahoto na PM News ya yi ikirarin cewa Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na kasa ya yi murabus daga ofishinsa.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jaridar ta ambaci rahotanni da dama, ciki har da Western Post, wacce ta ce yana da kusanci da shugabannin APC, a matsayin majiyarta.

Sanata Abdullahi Adamu
Ana ta kus-kus na cewa Abdullahi Adamu ya yi murabus. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Ta kara da cewa Adamu, tsohon gwamnan jihar Nasarawa, ya yi murabus da kansa don gudun a kore shi.

Jaridar ta kuma yi ikirarin cewa an tilastawa Adamu yin murabus ne saboda matsaloli daban-daban, ciki har da rashin goyon bayan Shugaba Bola Tinubu yayin kamfe da zargin bannatar da kudin jam'iyya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar PM News, wasu masu ruwa da tsaki a APC sun dade suna kira da cewa Adamu ya yi murabus ko kuma su tsige shi a taron Majalisar Zartarwa na Jam'iyyar, NEC, a wannan makon idan bai yi murabus ba.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Shugaban APC Ya Hakura da Rikon Jam’iyya, Ya Sauka Daga Kujerarsa

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa da farko an shirya yin taron ne a ranar 10 da 11 na watan Yuli amma aka dage zuwa ranar Talata da Laraban wannan makon saboda tafiye-tafiyen kasashen waje da Shugaban Kasa ya yi.

New Telegraph shima ma ta ruwaito rahoton cewa wai shugaban na APC ya yi murabus.

Shin shugaban na APC, Adamu Abdullahi ya yi murabus da gaske?

A lokacin hada wannan rahoton, Sanata Adamu bai riga ya fitar da sanarwar cewa ya yi murabus din da ake zargi ba.

Kuma, shugabannin jam'iyyar APC ba su fitar da ko wane irin rahoto a sahihan shafunkansu kan abin da ake zargin ya faru.

PM News, a rahotonta, ita ma ta ce sakataren watsa labarai na kasa na APC, Felix Morka, bai riga ya sakon neman karin haske da aka masa ba kan murabus din na Adamu.

Abin Lura: Wannan labari da ake dakon karin bayani a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164