Biliyan 500 Na Kayan Rage Radadi: Gwamnan Kano Ya Karyata Batun Sukar Tinubu
- Gwamnatin jihar Kano ta karyata rahotannin da ke yawo cewa ta soki tsarin rabon tallafin naira biliyan 500 na shugaban kasa Bola Tinubu
- Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam-Gwarzo, ya ce an yi wa jawabin da ya yi mummunan fassara ne
- Gwamnatin Abba Gida Gida ta jadadda cewar za ta ci gaba da ba manufofin Tinubu goyon baya don hadin kai da zaman lafiyar kasar
Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da rahotannin cewa ta soki tsarin rabon naira biliyan 500 na rage radadi da Shugaban kasa Bola Tinubu.
Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam-Gwarzo, ne ya yi karin hasken a cikin wata sanarwa da sakataren labaransa, Ibrahim Shauibu, ya saki a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli, a Kano, jaridar Premium Times ta rahoto.
Ba a fahimci jawbain gwamnatin Kano bane
Ya ce rahoton ya yi ikirarin karya cewa mataimakin gwamnan ya soki gwamnatin Tinubu kan raba naira miliyan 500 domin tallafawa masu kananan sana'o'i ta bankin masana'antu, rahoton Vanguard.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwar ta ce:
"Gwarzo ya yi tsokaci ne a wani bangare na labarai da ya kalla a safiyar ranar Alhamis tare da Sanata Ali Ndume, wanda ya nuna damuwarsa kan tsarin rabon kudin.
“Mataimakin gwamnan ya yi tsokaci ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar hadin gwiwa ta Kano a gidan gwamnatin Kano, yayin da suke bikin ranar hadin gwiwa ta duniya ta 2023.
"Babu a inda jawabin mataimakin gwamnan ya ambaci sunan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
"An shirya tsarin rabon kudin tun ma kafin shugaban kasa Tinubu ya kama aiki.
"Saboda haka, an yi wa furucin Gwarzo fassara a baibai ne, inda aka kasa fahimtar ainihin bayanin nasa."
Sanarwar ta kuma nakalto Gwarzo ya sake jaddada jajircewar gwamnati karkashin shugabancin Gwamna Abba Kabir-Yusuf wajen ci gaba da marawa manufar shugaban kasa Tinubu baya domin hadin kai da zaman lafiyan Najeriya.
Cire Tallafi: Abba Gida Gida Ya Soki Tinubu Kan Tsarin Rabon Kudi, Ya Bayyana Matsayar Shi A Kai
Idan za ku tuna, an rahoto a baya cewa gwamnatin jihar ta soki tsarin ba da tallafin da Shugaba Tinubu ya ke shirin yi na N500bn.
An tattaro cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya ce babu adalci a rabon inda jihar Lagos za ta kwashe kashi 47 sai yankin Kudu maso Kudu da kaso 17, inda sauran yankuna za su kwashi abin da ya rage.
Asali: Legit.ng