Mataimakin Shugaban Kasa Ya Gana Da Tsoffin Sanatoci a Villa, Ya Roki Abu 1

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Gana Da Tsoffin Sanatoci a Villa, Ya Roki Abu 1

  • Kashim Shettima ya karbi bakunci wakilan mambobin majalisar dattawa ta 9 da ta gabata a fadar shugaban kasa ranar Jumu'a
  • Mataimakin shugaban kasan ya bukaci su taimaka wa gwamnatin Tinubu wajen aiwatar da tsare-tsaren da ta zo da su
  • Sanatocin sun bayyana cewa sun gana da Shettima ne domin jaddada goyon baya da taya shi murnar kama aiki

FCT Abuja - Mataimakin shugban kasa, Kashim Shettima, ya yi kira ga 'yan Najeriya baki ɗaya daga kowane tsagin siyasa da su goyi bayan tsaruka da shirye-shiryen gwamnatin Bola Tinubu.

Shettima ya yi wannan kira ne ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuli, 2023 lokacin da ya karbi baƙuncin wasu daga cikin mambobin majalisar dattawa ta 9 da ta gabata.

Shettima da wasu mambobin majalisar dattawa ta 9.
Mataimakin Shugaban Kasa Ya Gada Da Tsoffin Sanatoci a Villa, Ya Roki Abu 1 Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsoffin Sanatocin sun kai ziyara ta musamman ga Shettima a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

"Tun Asali Abu 2 Ke Ya Kawo 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya" Tsohon Gwamna Ya Fasa Ƙwai

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran ofishin mataimakin shugaban kasa, Olusola Abiola, ya fitar, an ji Shettima na ƙara gode wa Sanatocin bisa haɗin kan da suke bayarwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma tabbatar wa tsoffin mambobin majalisar tarayya cewa, "Zai ci gaba da ba su goyon baya da kuma haɗin kai."

Menene makasudin ganawar Sanatocin da Shettima?

Da yake hira da yan jaridan gidan gwamnati jim kaɗan bayan gana wa da mataimakin shugaban ƙasa, jaggoran tawagar sanatocin, Sanata Ibrahim Oloriegbe ya ce:

"Mun zo nan ne domin taya mataimakin shugaban masa nurna, wanda yana ɗaya daga cikin mu, mu taya shi murnar kama aiki kuma mu yi addu'a ga shugaban kasa da shi kansa, gwamnatinsu ta cimma nasara."
"Haka nan mun zo nan mu kara jaddada goyon bayanmu a matsayin 'yan Najeriya kuma jagorori kuma 'ya'yan jam'iyyar APC cewa muna tare da gwamnati, za mu bada gudummuwa daidai gwargwado."

Kara karanta wannan

Babban Jigon PDP Ya Gana da Shugaba Tinubu a Villa, Ya Yi Magana Kan Sauya Sheƙa Zuwa APC

"Mun kuma yi amfani da wannan damar wajen miƙa godiya ga mataimakin shugaban ƙasa bisa naɗa ɗaya daga cikinmu a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa."

Wasu daga cikin waɗanda suka halarci gana wa da Shettima

Sauran mambobin tawagar wakilan sun kunshi, sanata Ibrahim Danbaba daga Sakkwato, Suleiman Kwari daga Kaduna, Yakubu Oseni daga Kogi da Hezekiah Dimka daga Filato.

Sauran sun haɗa da Lawal Anka daga Zamfara, Nora Daduut daga Filato, Kola Balogun daga Oyo, Kabir Barkiya daga Katsina Oriolowo Adelere daga Osun da Ibrahim Gobir daga Sakkwato.

Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Sabon Naɗi a Gwamnatinsa

A wani labarin kuma Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu , ya tabbatar da naɗin Taiwo Oyedele a mukami mai matuƙar muhimmanci.

Tinubu ya kafa sabon kwamiti da nufin magance kalubalen da suka yi katutu kan tsarin kasafi da kuma karban haraji a Najeriya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Wasu Manyan Jiga-Jigan PDP 2 a Aso Villa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262