Bidiyon Dala: 'Bita Da Kullin Siyasa Ne', Kakakin Ganduje Ya Yi Martani Kan Gayyatar Da Aka Yi Masa
- Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da karɓar korafe-korafe ta jihar Kano (PCACC) ta sake tado da batun bidiyon dala
- Hukumar ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya zo ya kare kansa dangane da zargin da ake masa
- Tsohon Kwamishina a lokacin Ganduje, Muhammad Garba, ya bayyana cewa hakan duk bita da ƙulli ne na siyasa
Kano - An bayyana cewa gayyatar da aka yi wa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje kan faifan bidiyon dala a matsayin wani shiri na siyasa.
An bayyana cewa an yi hakan ne domin daƙile batun muƙamin da ake sa ran Shugaba Bola Tinubu zai bai wa tsohon gwamnan.
Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar Alhamis ne shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta jihar Kano, ya gayyaci Ganduje ofishinsa don kare kansa kan bidiyonsa na dala.
Kwamishinan Ganduje ya ce gayyatar da aka yi masa siyasa ce kawai
Sai dai Muhammad Garba, tsohon kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na gwamnatin Ganduje, ya bayyana cewa hakan duk siyasa ce kawai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Garba wanda shi ke magana da yawun Ganduje, ya bayyana cewa an bijiro da duk waɗannan batutuwa a wannan gaɓar ne, don kawai a ɓata sunansa ganin cewa Tinubu ka iya ba shi muƙami.
Ya ce waɗanda suka bijiro da batun ba sa jin daɗin kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Ganduje da Tinubu, a cewarsa wannan ne dalilin yasa suke neman ɓata alaƙar.
Suna bakin cikin Ganduje zai samu muƙami
Garba ya ƙara da cewa mutanen suna baƙin cikin muƙamin da Ganduje zai samu a matakin tarayya ne, wanda zai ci gaba da amfanar mutanen Kano da shi.
Sai dai ya bayyana cewa ba su damu da duk wasu ƙulle-ƙulle da ake yi ba saboda Allah ne ke jujjuya komai.
A kalamansa:
"Amma bamu damu ba domin Allah ne kadai zai iya yanke abinda mutum zai samu da kuma lokacin da zai samu, kuma Allah ne zai yanke matakin da Ganduje zai taka a gaba, ko ya samu muƙami ko akasin haka."
PM News ta kawo rahoto cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da karɓar korafe-korafe ta jihar Kano (PCACC), ta gayyaci Ganduje domin ya amsa tambayoyi.
Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta shawarci Ganduje da ka da ya amsa gayyatar da aka yi masa.
Abba ya tura karin sunayen mutane 3 majalisa don naɗa su kwamishinoni
Legit.ng ta kawo muku wani rahoto kan cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aika da ƙarin sunayen mutane uku majalisar jihar don a tantancesu kan muƙaman kwamishinoni.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ke ƙorafin cewa an waresu a gefe wajen rabon muƙamai.
Asali: Legit.ng