Abba Gida Gida Ya Tura Sunayen Karin Kwamishinoni 3 Ga Majalisar Dokokin Jihar Kano

Abba Gida Gida Ya Tura Sunayen Karin Kwamishinoni 3 Ga Majalisar Dokokin Jihar Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf da ake kira da Abba Gida Gida na jihar Kano, ya sake aika wa da sunayen mutane 3 majalisar dokokin jihar
  • Mutanen dai na cikin waɗanda gwamnan ke son naɗawa kwamishinonin da za su yi aiki tare da shi a wa'adin mulkinsa
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan wasu ƙananan hukumomi a jihar ke ƙorafin cewa an barsu a baya wajen kujerun kwamishinonin

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Gida Gida ya aikawa da Majalisar Dokokin jihar sunayen ƙarin wasu mutane uku da yake so ya naɗa kwamishinoni a jihar.

Hakan dai na zuwa ne bayan ƙorafin da 'yan wasu ƙananan hukumomin suka yi, na cewa an ware su gefe guda wajen ba da kujerun kwamishinonin.

Abba ya tura sunayen karin mutane uku majalisar Kano
Abba Gida Gida ya aika da karin sunayen mutane uku da yake son ba mukamin kwamishina zuwa Majalisar jihar Kano. Hoto: Salisu Yahaya Hotoro
Asali: Facebook

Kakakin majalisar jihar ya bayyana sunayen kwamishinonin

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Jam'iyyar APC Ta Tsoma Baki Kan Bidiyon Dala, Ta Aike da Sako Ga Ganduje

Jibril Isma'il Falgore, Kakakin Majalisar Dokokin jihar Kano ne ya bayyana batun ƙarin sunayen da gwamnan ya turo ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ƙarin mutane ukun da Abba Gida Gida ke son naɗawa sun fito ne daga ƙananan hukumomin Dala, Fagge da kuma Nasarawa da ke cikin birnin Kano.

An bayyana sunayen mutanen da Ibrahim Ali Namadi daga Dala, Farfesa Ibrahim Jibrin daga Fagge, da kuma Amina Abdullahi Sani wacce 'yar ƙaramar hukumar Nasarawa jihar Kano ce.

Mai taimakawa Abba Kabir Yusuf ya yi martani kan sabbin kwamishinonin

Babban mai taimakawa Gwamna Abba Gida Gida a kafafen sada zumunta Salisu Yahaya Hotoro, ya wallafa saƙon taya murna ga sabbin kwamishinonin a shafinsa na Fesbuk.

Wani rubutu na Salisu da Legit.ng ta ci karo da shi a shafin nasa yana cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina Ya Naɗa Mataimaki Na Musamman Kan Harkokin 'Yan Gudun Hijira Na Jihar

“A madadin kafatanin masu amfani da kafafen sadarwa na zamani da ke faɗin jihar Kano, ofishin babban mataimaki ga gwamnan jihar Kano akan kafafen sadarwa na zamani yana taya Hajiya Amina S. Abdullahi (HOD), Hon. Ibrahim Namadi Dala da Prof. Ibrahim Jibrin Fagge (Provost) murnar zaɓo su da mai girma gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf yayi a matsayin sabbin kwamishinoni kuma yan majalisar zartarwa ta jihar Kano."
“Muna addu'a Allah Ubangiji ya basu ikon sauke wannan nauyi na al'ummar jihar Kano da aka ɗora musu.”

Hukumar yaƙi da rashawa ta jihar Kano ta gayyaci Ganduje kan bidiyon dala

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton cewa Hukumar karɓar korafe-korafe Da Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa ta jihar Kano (PCACC), ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.

Hukumar ta bayyana cewa ta gayyaci Ganduje ne domin ya amsa tambayoyi dangane da bidiyon dala da hukumar ke bincike a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng