Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Naɗe-Naɗen Da Aminu Tambuwal Ya Yi

Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Naɗe-Naɗen Da Aminu Tambuwal Ya Yi

  • Gwamnanati mai ci ta jihar Sokoto, ta kafa wani kwamiti da zai binciki muƙamai da naɗe-naɗen da gwamnatin baya ta yi
  • Kwamitin zai binciki sauya sunayen manyan makarantu da wasu naɗe-naɗen sarautun gargajiya da gwamnatin Tambuwal ta yi
  • Gabanin miƙa mulki ga sabuwar gwamnati, Tambuwal ya sauyawa wasu muhimman wurare sunaye da sunayen wasu manyan jihar Sokoto

Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu, ya kafa kwamitin mutane tara da zai duba duk wasu naɗe-naɗe da tsohon gwamnan jihar, Aminu Tambuwal ya yi a gab da ƙarshen gwamnatinsa.

Kwamitin ƙarƙashin jagorancin tsohon ministan harkokin ‘yan sanda, Malami Dingyadi, an ba shi aikin duba naɗin wasu sarautu na gargajiya da kuma sauya sunayen manyan makarantu da Tambuwal ya yi.

Hakan na ƙunshe ne a sanarwar da Malam Abubakar Bawa, sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Sokoto ya fitar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Niger Ya Gwangwaje Alhazan Jihar Da Kyautar Makudan Kudade, Ya Daukar Musu Muhimman Alkawura 3

Gwamnatin Sokoto za ta binciki wasu daga cikin ayyukan Tambuwal
Gwamnatin Sokoto za ta binciki naɗe-naɗen da Tambuwal ya yi. Hoto: Abubakar Rabi'u Range / Mustapha Sule Lamido
Asali: Facebook

Kwamitin gwamnan Sokoto zai duba batun sauya sunayen manyan makarantu

Sanarwar wacce aka fitar a ranar Litinin, ta kuma ce kwamitin zai duba batun sauyawa makarantu wuri, da naɗin shugabanninsu da gwamnatin da ta shuɗe ta yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar sanarwar:

“Za kuma su sake duba duk wasu naɗe-naɗe na gargajiya da tsohon gwamna Aminu Tambuwal ya yi a baya-bayan nan tare da magance korafe-korafen da aka yi kan wasu daga cikin waɗanda aka naɗa.”

Gwamna Ahmad Aliyu ya soke naɗe-naɗen da Tambuwal ya yi

A lokacin da Aliyu ya hau karagar mulki ya soke naɗin sarautun gargajiya da abin ya shafa tare da bayar da umarnin soke sauya sunayen manyan makarantun.

Rahoton The Guardian ya ce gwamnan ya kuma rushe shugabannin manyan ma'aikatu da sauran hukumomin jihar.

Mambobin kwamitin da aka sun haɗa da Bature Shinkafi, Dakta Kulu Abubakar, Isa Sadiq-Achida, Suleiman S/Fulani, da Dakta Umar Yabo a matsayin Sakatare, da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Ziyarci Sarkin Musulmi, Ya Nemi Alfarma 1 Tak

Tambuwal ya karrama manyan malamai da shugabannin jihar Sokoto

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya Legit.ng ta kawo muku wani rahoto kan cewa, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya karrama wasu manyan malamai da shugabanni a jihar.

Tambuwal ya karrama su ne ta hanyar sauya sunayen wasu muhimman wurare da sunayen waɗannan malamai da shugabannin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng