Bola Tinubu Zai Dawo Najeriya Yau, Akwai Yiwuwar a Nada Ministoci Bayan Sallah

Bola Tinubu Zai Dawo Najeriya Yau, Akwai Yiwuwar a Nada Ministoci Bayan Sallah

  • Nan da ‘yan kwanaki, Bola Ahmed Tinubu zai cika wata guda da hawa kan kujerar shugaban kasa
  • Da zarar ya dawo daga kasar waje ake tunanin zai aikawa majalisar dattawa jerin sunayen Ministocinsa
  • Tinubu zai yi idi a Legas, Sanatoci za su iya fara aikin tantance Ministoci bayan hutun babbar sallah

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Landan a kasar Ingila, ya zo Najeriya a ranar Talata domin shirin bikin babbar sallah da za ayi a gobe.

A safiyar Talatar ne rahoto ya fito daga Punch cewa jirgin shugaban kasar zai dawo gida bayan shafe kwana da kwanaki tsakanin Faransa da Ingila.

A jiya wasu na kusa da fadar shugaban kasa sun shaida cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai dawo Najeriya, ya yi sallah a gidansa a Ikoyi a Legas.

Kara karanta wannan

Tsohon Ministan Jonathan Ya Ajiye Babban Mukami Na Duniya Saboda Nadin Tinubu

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Rt Hon Femi Gbajabiamila Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Bola Tinubu zai yi idi a mulki

Wannan ce sallar farko da Bola Tinubu zai yi a matsayin shugaban kasa, ya zabi ya yi bikin idin a mahaifar ta Legas a maimakon babban birnin tarayya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akwai yiwuwar shugaban kasar ya halarci filin idin Obalende da yake barikin Dodan a Legas. A shekarun baya, nan ne ya kasance fadar shugaban Najeriya.

Kafin Muhammadu Buhari ya bar kan mulki, ya bada umarni a maida wannan filin idi ya bar hannun gwamnatin tarayya, ya koma karkashin jihar Legas.

Bayan ya yi sallar idi a filin da yanzu yake karkashin kungiyar Jama’atul Muslimeen, rahoton ya ce Tinubu ba zai koma aiki a Aso Rock a ranar Juma’ar ba.

Sintiri zai ragu a fadar Aso Rock

Watakila Mai girma shugaban kasar ya yi zamansa a gida har zuwa Litinin kafin ya wuce Aso Rock. Hakan zai ba shi damar ya gujewa hayaniyar mulki.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Haɗu da Shugaban Kasar Benin, Ya Taɓo Batun Iyakoki da Kasuwanci

Daga mako mai zuwa ake sa ran majalisar dattawa za ta iya karbar jerin sunayen wadanda shugaban na Najeriya ya zaba domin su zama Ministocinsa.

A dokar kasa, sai Sanatoci sun tantance Ministocin kafin a raba masu ma’aikatu, har su fara aiki. Legit.ng Hausa ta fahimci an fara shirin kafa gwamnati.

Wata majiya ta ce a halin yanzu an gama aiki a kan Ministocin, abin da ya rage kurum shi ne ‘yan majalisa su fara shirin tantance su a makon gobe.

Nadin sababbin hafsun tsaro

A baya rahoto ya zo cewa Shugaban sojojin kasa, Taoreed Lagbaja ya shiga ofis, ya canzawa manyan sojojin Najeriya wuraren aiki a barikoki da Hedikwata.

Janar Taoreed Lagbaja ya nada sabon kwamandan makarantar NDA da shugaban makarantar koyon yaki da duk wadanda za su jagoranci Dakarun kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng