Rikici Ya Barke a Benue Yayin da Shugabannin Kananan Hukumomi 23 Suka Tashi Tsaye a Kan Gwamna Alia

Rikici Ya Barke a Benue Yayin da Shugabannin Kananan Hukumomi 23 Suka Tashi Tsaye a Kan Gwamna Alia

  • Shugabannin kananan hukumomi 23 a jihar Benue sun sha alwashin kin bin umurnin gwamnatin jihar na barin ofishoshinsu
  • A cewar fusatattun ciyamomin, zabarsu aka yi a kan kujerarsu, don haka ba za su iya mika mulki ga jami'i mafi girma a kananan hukumominsu mabanbanta ba
  • Da yake martani, gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya ce maganar dakatar da shugabannin kananan hukumomin na nan har sai an kammala bincike a kansu

Shugabannin kananan hukumomi 23 na jihar Benue sun nunawa Gwamna Hyacinth Alia yatsa.

A ranar Asabar, 24 ga watan Yuni, fusatattun shugabannin kananan hukumomin sun sha alwashin kin bin umurnin Gwamna Alia kan dakatar da su daga ofis, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia
Rikici Ya Barke a Benue Yayin da Shugabannin Kananan Hukumomi 23 Suka Tashi Tsaye a Kan Gwamna Alia Hoto: Benue state government
Asali: Facebook

Sakamakon shawarar da majalisar dokokin jihar ta ba Gwamna Alia na dakatar da shugabannin kananan hukumomi 23 domin bayar da damar gudanar da bincike a harkokin kudadensu, hukumar kula da harkokin kananan hukumomi da sarauta (BLGCA) a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni, ta umurci ciyamomin da su mika mulki ga manyan jami'ai a hukumominsu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Dakatar da Ciyamomin Kananan Hukumomi 23, PDP Ta Maida Martani Mai Zafi

Shugabannin kananan hukumomi 23 sun nunawa Gwamna Alia na Benue yatsa

Sai dai da suke martanin gaggawa a wani taron manema labarai a ranar Asabar, shugabannin kananan hukumomin sun bayyana cewa ba za su ba umurnin yan majalisar ko na hukumar BLGCA hadin kai ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mike Uba, shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi na Najeriya (ALGON), reshen jihar Benue wanda ya yi magana a madadin takwarorinsa, ya ce ba za su mika kai ga rashin ka'ida domin yin hakan zai zama illa ga jihar.

Ya ce zabarsu aka yi a kan kujerarsu tare da kansilolinsu a ranar 30 ga watan Afrilun 2022 na tsawon shekaru biyu wanda zai kare a ranar 30 ga watan Afrilun 2024.

"Har yanzu ku dakatattu ne", Gwamnan Benue ya yi martani ga fusatattun shugabannin kananan hukumomi

Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya ce har yanzu shugabannin kananan hukumomi 23 na jihar Benue dakatattu ne har sai an kammala bincike a kansu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Kori Ma'aikata Daga Bakin Aiki Bayan Wani Shugaban Makaranta Ya Aikata Abu 1

Ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga ikirarin shugabannin kananan hukumomin a taron manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni, rahoton Daily Trust.

Majalisar Dokokin Jihar Benue Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomi 23

Legit.ng ta kawo a baya cewa majalisar dokokin jihar Benue ta bayar da shawarar dakatar da shugabannin kananan hukumomi 23 a jihar a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni kan zargin karkatar da kudade.

Kakakin majalisar, Aondona Dajoh, ne ya sanar da shawarar a yayin zaman majalisar bayan ya duba rahoton kwamitin wucin gadi da aka kafa domin binciken rahoton kudaden shiga da kudaden da aka kashe wanda gwamnan ya gabatar masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng