“Za a Yi Kukan Murna a Wannan Gwamnati Na Tinubu”: Malamin Addini Ya Yi Hasashe
- Fitaccen faston Najeriya, Prophet Jeremiah Omoto Fufeyin ya bayyana makomar yan Najeriya cikin watanni shidan farko na gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu
- Malamin addinin ya yi tinkaho cewa ya yi hasashen zuwa shugaban kasa Tinubu a Nuwamban 2022
- A cewarsa, yan Najeriya za su yi kukan farin ciki cikin watanni shidan farko na gwamnatin shugaban kasa Tinubu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Prophet Jeremiah Omoto Fufeyin na cocin Christ Mercyland Deliverance Ministry ya yi hasashen cewa yan Najeriya su tsammaci tarin ci gaba a watanni shida masu zuwa na gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu.
Ku tuna cewa Bola Tinubu ya dauki rantsuwar aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu bayan karewar wa'adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Prophet Fufeyin ya bayyana sakon Ubangiji game da watanni shidan farko na gwamnatin Shugaban kasa Tinubu
Tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16, mutane da dama na ta hasashe a kan gwamnatinsa bisa la'akari da yawan manufofin da ya aiwatar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da ya garzaya shafinsa na Facebook a karshen makon jiya, Prophet Fufeyin ya yi hasashen abun da yan Najeriya za su tsammaci gani daga sabuwar gwamnatin nan da watanni shida masu zuwa.
Malamin ya yi tinkaho cewa duk faston da kalamansa basu faru ba bai kamata a dunga daukarsa a matsayin babban fasto ba, yana mai cewa ya yi hasashen nasarar jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Yadda na yi hasashen nasarar Tinubu a 2022, Prophet Fufeyin ya magantu
Ya tuna yadda ya yi hasashen a watan Nuwamba da kuma chanjin da kasar za ta fuskanta cikin watanni shida na gwamnatin Tinubu.
Fufeyin ya ce:
"Ina mai sake yi maku hasashe, a wannan wa'adi na Tinubu, za a yi kukan farin ciki a Najeriya cikin watanni shida masu zuwa. Ba za a yi bakin ciki ba, kuma Najeriya mai inganci na zuwa. Ka sanar da sauran mutane wannan hasashe sannan ka kasance cikin albarka."
Girman kan Tinubu zai kai shi ya baro, Inji Charly Boy
A wani labari na daban, mawakin Najeriya Charles Oputa wanda aka fi sani da Charly Boy ya yi martani a kan tsige shugabannin tsaro da nada sabbi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi.
A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, Charly Boy ya nuna rashin jin dadinsa ga yan Najeriya da suke jinjinawa shugaban kasar kan yadda yake tafiyar da harkokin gwamnati a baya-bayan nan.
Asali: Legit.ng