Rusau A Kano: Mun Kwato Filayen Tiriliyoyin Nairori, Gwamnatin Kano Ta Yi Karin Bayani

Rusau A Kano: Mun Kwato Filayen Tiriliyoyin Nairori, Gwamnatin Kano Ta Yi Karin Bayani

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta ƙwato filaye da darajarsu ta haura tiriliyan daga lokacin da ta ƙaddamar da rushe-rushen da take yi
  • Gwamnatin ta Abba Gida Gida ta rushe wasu gine-gine a wurare daban-daban da suka haɗa da Daula Otal, filin Idi, cikin kasuwannin Kwari da Wambai da sauransu
  • Gwamnatin ta kuma zargi gwamnatin da ta shuɗe da siyar da filayen gwamnati don biyan buƙatun kai, zargin da tsohon gwamnan ya musanta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ƙwato filayen da darajarsu ta kai tiriliyoyin nairori tun bayan da ta fara aikin rusau a wasu wurare a faɗin jihar.

Sakataren gwamnatin jihar ta Kano, Dakta Abdullahi Baffa Bichi ne ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels.

Abdullahi Bichi ya ce sun ƙwato filaye na sama da tiriliyon ɗaya
Abdullahi Baffa Bichi ya ce gwamnatinsu ta ƙwato filaye na tiriliyoyin nairori. Hoto: Gida-Gida TV
Asali: Facebook

Abba Gida Gida ya rushe manyan gine-gine da dama a birnin Kano

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Mayar Wa Abba Gida-Gida Martani: Na Kashe Sama Da Biliyan 20 Kan Tallafin Karatu

Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta rusa wasu gine-gine da suka haɗa da a Otal ɗin Daula, filin Idi, cikin kasuwannin Kwari da Wambai da dai sauransu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta kuma zargi gwamnatin da ta shude da yin sama da faɗi da dukiyar ƙasa, duk da dai tsohon gwamna jihar ta Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa zargin ba shi da tushe.

Daily Trust ta wallafa inda Abdullahi Bichi yake cewa:

“Na ji wani na iƙirarin cewa an ruguza gine-gine na naira biliyan 129.”
“Mun kwato kadarori (filaye) na jihar Kano da darajarsu ta kai tiriliyan da gwamnatin da ta gabata ta karkatar ga kansu da iyalansu. Filin Idi kaɗai ya kai tiriliyan.”

Wata kungiya ta nemi gwamnatin Kano da ta dakatar da rushe-rushen da take yi

Legit.ng a baya ta kawo muku cewa wata ƙungiyar masu tsara birane, NITP, ta yi kira ga sabon gwamnan jihar Kano, Abba Gida Gida, da ya dakatar da rushe-rushen da yake gudanarwa a yanzu.

Kara karanta wannan

Rusau Da Wasu Muhimman Matakai Da Gwamnoni Suka Dauka a Cikin Kwana 20 Da Hawa Mulki

Ƙungiyar ta bayyana cewa rusau da gwamnatin ke ci gaba da yi na janyowa mutane mummunar asara.

Ganduje ya mayarwa da Abba Martani kan tallafin karatu

A wani labari da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa, tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi wa Abba Gida Gida zazzafan martani kan ba da tallafin karatu.

Gamduje ya musanta batun da Abba ya yi na cewa ba a bayar da tallafin karatu ba a lokacin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Tags: