Yanzu Yanzu: Tajudeen Abass Ya Zama Kakakin Majalisar Wakilai
- An ayyana Abbas Tajudeen a matsayin sabon kakakin majalisar wakilai a ranar Talata, 13 ga watan Yuni
- Benjamin Kalu, dan majalisa mai wakiltan mazabar Bande ta jihar Abia, ya zama mataimakin kakakin majalisar wakilai
- Kafin ayyana shi, Alhassan Doguwa ya zabi Abbas don zama kakakin majalisar wakilan
Bayan fafatawa mai zafi, daga karshe dai Hon. Abbas Tajudeen ya zama kakakin majalisar wakilai.
Haka kuma, Hon. Benjamin Kalu, dan majalisa mai wakiltan mazabar Bende ta jihar Abia ya zama mataimakin kakakin majalisar wakilai.
Hon Abass ne sabon kakakin majalisar wakilai
Abbas, wanda jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ke so ya yi nasarar darewa kujerar kakakin majalisa bayan ya samu mafi rinjayen kuri'un zababbun yan majalisa a ranar Talata, 13 ga watan Yuni.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sashin Hausa na BBC ya kuma rahoto cewa Tajudeen Abbas ya kayar da Idris Wase da Aminu Sani Jaji bayan lashe kusan dukkanin kuri'un majalisar wakilan.
Da farko, 68 daga cikin zababbun yan majalisar wakilai 72 daga yankin kudu maso yamma sun marawa Tajudeen Abass da Benjamin Kalu baya a matsayin kakakin majalisa da mataimakin kakakin majalisar wakilai ta 10.
Majalisa ta 10: Sanata Godswill Akpabio ya karbi rantsuwar aiki a matsayin shugaban majalisar dattawa
A gefe guda, mun ji cewa tsohon ministan Neja Delta kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio, ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban majalisar dattawa.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an rantsar da Sanata Akpabio ne bayan ya samu nasarar lallasa abokin karawarsa, Sanata Abdul'aziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara.
Akpabio ya samu kuri'u 63 a zaben da aka gudanar da safiyar Talata, 13 ga watan Yuni, 2023, yayin da Sanata Yari ya tashi da ƙuri'u 46.
Shugaban majalisar dattawa: Zababbun Sanatoci za su siyar da kuri'unsu $5,000, $10,000 ko fiye da haka
A wani labarin, mun ji cewa yayin da ake shirye-shiryen rantsar da majalisar dokokin tarayya ta 10 a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, bayanai sun nuna zababbun sanatoci na kokarin siyar da kuri'unsu ga masu neman takarar shugabancin majalisar.
A majalisar dattijai, yan takara sun fara kokarin zawarcin yan majalisa don marawa kudirinsu na son darewa kujerar shugaban majalisar dattawan baya.
Asali: Legit.ng