Rusau: Kada Ka Lalata Ayyukan Ganduje a Kano, Kungiyar APC Ta Gargadi Abba Gida-Gida

Rusau: Kada Ka Lalata Ayyukan Ganduje a Kano, Kungiyar APC Ta Gargadi Abba Gida-Gida

  • Kungiyar goyon bayan APC ta magantu a kan aikin rusau da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke ci gaba da yi a jihar Kano
  • Kungiyar ta zargi Gwamna Abba Gida-Gida da kokarin lalata ayyukan da gwamnatin baya ta Abdullahi Ganduje ta bari da sunan rusau
  • Ta yi kira ga dattawan Kano musamman ubangidan sabon gwamnan, Rabiu Kwankwaso da su take masa burki tun kafin lokaci ya kure

Kano - An gargadi gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a kan lalata ayyukan da magajinsa, Abdullahi Umar Ganduje ya bari da sunan rusa gine-gine da basa bisa ka'ida a jihar.

Cikin kasa da makonni da kama aiki, gwamnan ya shiga aikin rusa gine-ginen da basa bisa ka'ida da kudadensu ya kai biliyoyin naira, Daily Trust ta rahoto.

Gwamna Abba ya ce za a ruguza gine-gine da basa bisa ka'ida wadanda aka yi a makarantu, masallatai, wuraren wasanni, makabartu, kasuwanni da asibitoci domin tabbatar da bin ka’idar gine-gine da kare jama’a.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Ci Gaba Da Aikin Rusau Bayan Zazzafan Musayar Yawu Da Aka Yi Tsakanin Ganduje Da Kwankwaso

Gine-ginen da aka rusa a Kano
Rusau: Kada Ka Lalata Tarihin Da Ganduje Ya Kafa a Kano, Kungiyar APC Ta Gargadi Abba Gida-Gida Hoto: Arewa
Asali: Facebook

Abba Kabir Yusuf na kokarin bata tarihin da Ganduje ya kafa ne a Kano, Kungiyar APC

Sai dai kuma kakakin kungiyar goyon bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) wato Progressive Foundational Movement (PFM), Jamilu Sani ya bayyana cewa manufar wani kokari ne na lalata ayyukan tsohon gwamna Ganduje.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sani ya bayyana cewa rusa otel din Daula da aka yi wanda a cewarsa ta hadin gwiwa ce tsakanin jihar da kamfani mai zaman kansa zai aike sako mara kyau ga masu son zuba hannun jari.

Ya ce:

"Muna matukar mamakin yadda ake gudanar da aikin rushe-rushe na rashin hankali a jihar Kano, abun damuwa ne ganin yadda mutane ke rasa kasuwancinsu da sunan rusau. Ta yaya za ka jefa mutane, talakawanka, a cikin irin wannan hali na kunci saboda ka tsani magajinka, Ganduje?

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP Ta Fusata, Ta Yi Martani Mai Zafi Kan Ganduje Bisa Barazanar Marin Kwankwaso

"Ganduje a matsayinsa na wanda ya zamanantar da Kano ya yi iya bakin kokarinsa ga jihar. Don haka, muna kira ga dattawan jihar, musamman ubangidan Gwamna Yusuf a siyasa, tsohon gwamna, Rabiu Musa Kwankwaso da ya saita gwamnan ya dawo cikin hankalinsa kafin lokaci ya kure.
"Muna so mu roki Gwamna Yusuf da ya mayar da hankali kan aikinsa maimakon shiga aikin lalata gagarumin tarihin da Ganduje ya kafa a jihar Kano."

Abba Gida-Gida ya ci gaba da rusau a Kano duk da sukar da yake sha

A gefe guda, mun ji a baya cewa gwamnatin Abba Gida-Gida ta koma bakin aikin da ta faro na rusa gine-ginen da aka yi a wuraren gwamnati da ake zargin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje da siyar da su.

Lamarin na zuwa ne yan kwanaki bayan tsoffin gwamnonin jihar, Rabiu Musa Kwankwaso da Ganduje sun yi musayar yawu kan rushe-rushen da ake yi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng