Jam'iyyar APC Ta Zabo Malamin Makaranta a Matsayin Dan Takarar Mataimakin Gwamna a Jihar Kogi
- Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kogi ta zaɓi malamin makarantar firamare a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna
- Mr Joel Salifu ya zama mataimakin ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar Usman Ododo, a zaɓen 11 ga watan Nuwamba
- Salifu ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen ganin jam'iyyar ta lashe zaɓen gwamnan da ke tafe nan gaba
Jihar Kogi - Ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Usman Ododo, ya sanar da malamin makarantar firamare, Salifu Joel, a matsayin mataimakinsa.
Jaridar Punch tace Joel yanzu haka shi ne shugaban ƙungiyar malamai ta ƙasa a jihar kuma ma'ajin ƙungiyar ƙwadago ra ƙasa a jihar Kogi.
Gwamnan jihar Yahaya Bello, ya sanar da cewa jam'iyyar APC ta zaɓo Mr Joel ne saboda tana son ta tafi da kowa a yunkurin da ta ke na ciyar da jihar gaba.
Shugaban jam'iyyar APC na jihar, Abdullahi Bello, ya taya Ododo da mataimakinsa murna sannan ya yabawa gwamnan jihar bisa yadda ya ke jagorantar jam'iyyar, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya yaba da zaɓin da aka yi wa Salifu Joel, wanda malamin makaranta ne saboda ya fito daga ɓangaren koyarwa wanda ya ke da matuƙar muhimmanci ga al'umma.
Joel ya nuna jindaɗinsa kan wannan matsayi da aka ba shi
"Bani da kalaman da zan yi amfani da su a matsayi na malamin makaranta, a zaɓo ni a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamna." A cewarsa.
"Lokacin da aka fara tuntuɓa ta, har cikin zuciya ta na amince na karɓi wannan matsayin, saboda daga Allah ne."
"Ina son bayar da tabbacin cewa zan yi duk abinda zan iya yi domin ganin jam'iyyar mu ta samu nasara a zaɓe mai zuwa."
Gwamna Bala Mohammed Ya Zama Sabom Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP
A wani rahoton na daban kuma, gwamnan jihar Bauchi, Bala.Mohammed ya zama sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP.
Gwamna Bala Mohammed ya maye gurbin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, daga shugabancin ƙungiyar gwamnonin na jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng