Dalilin Da Yasa Na Janye Karar Da Na Shigar Kotun Zabe – Al Makura

Dalilin Da Yasa Na Janye Karar Da Na Shigar Kotun Zabe – Al Makura

  • Sanata Umaru Tanko Al-Makura ya magantu bayan ya janye karar da ya shigar kotun zabe inda yake kalubalantar sakamakon zaben sanatan Nasarawa ta kudu
  • Tsohon gwamnan Nasarawa ya ce ya janye karar da ya shigar na kalubalantar nasarar Mohammed Ogboshi Onawo a zaben 2023 saboda wanzar da zaman lafiya a jihar
  • Al Makura ya ce ya dauki wannan matakin ne a matsayinsa na dan kasa mai kishi da son ci gaban Nasarawa da Najeriya baki daya

Nasarawa - Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Umaru Tanko Al-Makura, ya bayyana cewa ya janye karar da ya shigar gaban kotun zaben majalisar dokoki na tarayya da jiha da ke Lafia ne saboda samar da zaman lafiya a jihar.

A wata sanarwa da ya saki a garin Liafia kuma Daily Trust ta samu, Sanata Al-Makura ya yi bayani cewa ya janye daga shari'arsa da ke kalubalantar zaben Mohammed Ogboshi Onawo na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Kara karanta wannan

“Sai An Tauna Tsakuwa Idan Za a Kai Najeriya Gaba”: Wike Ya Goyi Bayan Tinubu Kan Cire Tallafin Mai

Sanata Umaru Tanko Almakura
Dalilin Da Yasa Na Janye Karar Da Na Shigar Kotun Zabe – Al Makura Hoto: The Sun
Asali: UGC

Siyasa ba abun a mutu ko ayi rai bace, Al Makura

Almakura ya bayyana cewa babu wata sadaukarwa da ta yi yawa domin dorewar zaman lafiyar jihar da Najeriya baki daya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanatan mai wakiltan yankin Nasarawa ta kudu a majalisar dokokin tarayya, ya bayyana cewa a matsayinsa na dan kasa mai kishin kasa, ya yanke shawarar yin sadaukarwar domin jihar da kasar su ci gaba.

A cewarsa, siyasa ba abun a mutu ko ayi rai bace kuma akwai bukatar sabonta fatan mutane domin samun makoma mai kyau.

Sanata Al-Makura wanda ya bayyana cewa shari'a na zuwa da sabani da dama da wasu rashin zaman lafiya a mulki, ya ce ya yanke shawarar janye shari'arsa a kotun zabe ne, biyo bayan rokon da sarakunan da sauran shugabanni suka yi masa.

Da farko dai sanatan ya kalubalanci ayyana Onawo a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Nasarawa ta kudu da aka yi yayin zaben da ya gabata a jihar, yana mai zargin magudi a wasu gudunmomi musamman a garin Lafia.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fara Mulki da Ciwon Kai, ‘Yan Kwadago Sun Sa Ranar Shiga Yajin-Aiki

Sai dai kuma, sanatan ya baiwa magoya bayansa mamaki ta hanyar da janye karar da ya shigar lokacin zaman kotun zabe, jaridar Leadership ta rahoto.

Yan daba sun farmaki ayarin motocin Gwamna Yahaya Bello

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu tsagerun mutane sun kai hari kan ayarin motocin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Lamarin ya afku ne a ranar Asabar, 3 ga watan Yuni, yayin da gwamnan ke a hanyarsa ta komawa Lokoja daga babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng