Buhari Ya Umurci Osinbajo Da Sauran Manyan Gwamnati Su Bayyana Kadarorinsu
- Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi fom din bayyana kadarorinsa gabannin barinsa mulki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu
- Ya ce shawarar da ya yanke na karbar fom din ita ce za ta tabbatar da gaskiya a cikin gwamnati
- Shugaba Buhari ya bukaci mukarrabansa da su bi sahunsa sannan su karbi takardar ayyana kadarorinsu
Abuja – Shugaban kasa Muhamnmadu Buhari ya umurci mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Atoni Janar na tarayya, Abubakar Malami da sauran mambobin majalisarsa da su bayyana kadarorinsu.
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, Shugaba Buhari ya yi umurnin ne a babban birnin tarayya a ranar Juma’a 26 ga watan Mayu.
Shugaban kasar ya kuma kasance mutum na farko da ya karbi fom din ayyana dukiyarsa daga wajen Farfesa Isah Mohammed, Shugaban hukumar CCB.
Jim kadan bayan karbar fom din, shugaba Buhari ya ce bin tsarin da kundin tsarin mulki ya tanadar na bayyana kadarorinsa shine mafi dacewa da dimokuradiyya, gaskiya da da’a da nufin ginawa da karfafa aikin gwamnati a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Vanguard ta rahoto Buhari yana cewa:
"Na sanya hannu kuma na karbi fom dina. Daga nan, zan bukaci manajan bakina a Kaduna da ya nuna mani duk abun da ya shiga da fita daga asusuna.
"Babu wanda aka daukewa ayyana kadarorinsu. Ina sa ran kowa daga mataimakin shugaban kasa har zuwa kasa su bi tsarin."
A halin da ake ciki, shugaban CCB, Farfesa Mohammed, ya jinjinawa shugaban kasar kan yadda yake bayar da hadin kai a kodayaushe.
Ya ce goyon bayan da Buhari ke ba hukumar ya sa kaso 99 cikin dari na zababbun jami'ai da wadanda aka nada suna ba da hadin kai.
Farfersa Mohammed ya kuma nuna godiyarsa kan taimakon da shugaba Buhari ya yi wajen taimakawa hukumar ta yadda take gudanar da aikinta cikin sauki kuma yadda ya kamata.
May 29: Buhari ya zagaya da Tinubu fadar Villa
A wani labarin, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zagaya da shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu don nuna masa fadar Villa.
Hakan ya kasance ne jim kadan bayan sun idar da sallar Juma'a a masallacin da ke fadar gwamnati.
Asali: Legit.ng