Jam'iyyar Labour Ta Dauki Matakin Hambarar Da Hukuncin Kotun Kano Na Soke Takarar Gwamnan Abia

Jam'iyyar Labour Ta Dauki Matakin Hambarar Da Hukuncin Kotun Kano Na Soke Takarar Gwamnan Abia

  • Lauyan jam'iyyar Labour Party, Umeh Kalu SAN, ya ɗaukaka ƙara inda ya nemi kotu ta yi watsi da hukuncin kotun Kano
  • Wata kotun tarayya da ke zamanta a Kano ce ta soke nasarar da gwamnan na Abia Alex Otti ya samu, inda ta ce zaɓen fidda gwanin Labour bai cika sharuɗa ba
  • Yanzu dai ana jira a ji hukuncin da kotun ɗaukaka ƙarar za ta yanke kan Ottin gabanin ranar da za a rantsar da zaɓaɓɓun shugabanni, wato 29 ga watan Mayu

Biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya a Kano ta yanke na soke zaɓen zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abia, Alex Otti, a zaɓen gwamnan jihar da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris, Labour ta daukaka kara.

Hukuncin kotun ya samo asali ne daga shari’a mai lamba FHC/KN/CS/107/2023 da Mista Ibrahim Haruna Ibrahim ya shigar a kan jam’iyyar Labour da kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, in ji Rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Amince Ya Mayar Wa Borno Naira Biliyan 16

Jam'iyyar Labour ta daukaka kara kan hukuncin da kotun Kano ta yanke
Jam'iyyar Labour ta daukaka kara kan hukuncin da kotun Kano ta yanke kan dan takararta Alex Otti. Hoto
Asali: Facebook

Zaben fitar da gwani na Jam'iyyar Labour ya saba ka'ida

Kotun ta yanke hukuncin cewa tsarin zaɓen da ya kai ga samun takarar zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abia, Alex Otti, da sauran ‘yan takarar jam’iyyar ta Labour, bai cika ƙa’idojin da aka gindaya ba a dokar zaɓe ta 2022.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da aka tabo a shari’ar, shi ne gazawar jam’iyyar Labour ta ƙasa wajen miƙa rajistar mambobinta ga INEC kwanaki 30 kafin zaɓukan fitar da gwani.

Kotu ta ce hakan ya saɓawa doka, wanda dalilin hakan, ɗaukacin zaɓen da aka gudanar ya ɓaci.

A jingine komai tukuna yanzu

Mai shigar da ƙarar ya nemi kotu da ta sa baki a jingine takardar shaidar cin zaɓe da aka bai wa ‘yan takarar jam’iyyar Labour.

Haka nan ya nemi kotu ta umarci INEC ta bayyana waɗanda ke biye a matsayin waɗanda suka yi nasara a dukkan mazabun da jam’iyyar Labour ta samu nasara.

Kara karanta wannan

Hotuna: Ɗan El-Rufai, Bello Ya Angwance Da Santaleliyar Amaryarsa a Abuja

Mai shari’a Yunusa ya bayyana cewa:

“Jam’iyyar da ba ta bi matakan dokar zaɓe ba, ba za a ce tana da ɗan takara a zaɓe ba, don haka ba za a iya bayyana cewa ita ce ta lashe zaɓen ba. Don haka, kuri’un da wanda ake kara (Labour Party) ya samu, kuri’u ne na banza.”

Kotu ta ki bada umarnin bai wa kowa satifiket

Channels TV ta ce alƙalin ya ƙi ba da umarnin a bai wa kowane ɗan takara takardar shaidar cin zabe a jihar ta Abia, sakamakon jam'iyyun da suka zo na biyu ba su shigar da ƙara a kotun ba.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Lauyan jam’iyyar Labour, Umeh Kalu, SAN, ya shigar da kara a ranar 22 ga watan Mayu, inda ya buƙaci kotun ta yi watsi da hukuncin da kotun ta Kano ta yanke.

Ba zaɓen gwamnan Abia kotu ta soke ba

Kara karanta wannan

Dan Takarar Gwamnan PDP a Ogun Ya Shiga Tasku, 'Yan Sanda Na Tuhumarsa Da Siyan Kuri'a Da N2bn

A wani labarin da muka wallafa a baya, kotun tarayya da ke Kano ta yi ƙarin haske kan hukuncin da ta yanke.

Kotun ta ce ba wai nasarar gwamnan Abia ta soke ba, takarar ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam'iyar Labour Party a Kano ta soke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng