Bikin Rantsar Da Tinubu: Abubuwa 7 Da Buhari Zai Yi a Satin Ƙarshe A Matsayin Shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shiga makonsa na ƙarshe a matsayin shugaban Najeriya yayin da yake shirin miƙawa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a ranar Litinin mai zuwa, 29 ga watan Mayu.
A makon ƙarshe na shugaba Buhari a matsayin shugaban Najeriya, zai gudanar da ayyuka da dama, wadanda aka bayyana su a matakai 7 kamar haka:
Ƙaddamar da matatar mai
A ranar Litinin, 22 ga watan Mayu ne shugaba Buhari zai ƙaddamar da matatar man Dangote da ke Legas, kwanaki 7 kafin ya mika mulki a hukumance.
A wannan rana kuma, shugaban ƙasa zai ƙaddamar da kamfanin Kajola Wagon, na dala miliyan 2.4 a jihar Ogun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bashir Ahmed, mai taimakawa shugaban ƙasar a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewa, wannan aiki shi ne irinsa na farko a nahiyar Afrika.
Haka nan kuma, aikin na cikin ayyuka 1 cikin 2 da gwamnatin kasar Sin ta bayar ta hannun kamfanin gine-gine na kasar Sin CCECC, domin bunƙasa harkokin jiragen ƙasa a Najeriya.
The Guardian ta dora a shafinta na Tuwita:
Duba jiragen ruwa
Har ila yau, Buhari zai halarci taron duba jiragen ruwa da rundunar sojin ruwa ta Najeriya za ta gudanar, inda rundunar za ta yi baje kolin jiragen yaƙi 16, da jirage masu saukar ungulu, da jiragen yaƙi domin karrama shugaban ƙasar.
Wannan dai wata al'ada ce da sojojin ruwa na duniya kan yi domin girmama shugabannin ƙasashensu.
Bayar da takardun miƙa mulki
A ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu, shugaban ƙasar mai barin gado zai mika takardum miƙa mulki ga zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a makon jiya, Juma’a, 19 ga watan Mayu, a wani taron manema labarai a Abuja.
Bayar da lambobin girmamawa ga Tinubu da Shettima
Daga cikin jerin sunayen da kwamitin miƙa mulki ƙarƙashin jagorancin Mustapha ya fitar a ranar Juma’a, Buhari zai ba da lambar girmamawa ta ƙasa ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito za a bawa Tinubu lambar girmamawa ta GCFR. Shi kuma Shettima za a karrama shi da lambar girmamawa ta GCON.
Liyafar cin abinci da sashen rundunar sojoji ga PMB
Haka zalika, sojojin Najeriya za su gudanar da wata liyafar cin abincin dare ta bankwana ga shugaba Buhari mai barin gado. Wannan ma wata al'ada ce ta karrama shugaba.
An dai shirya shagalin ne domin karrama shugaba Buhari a yayin da zai bar fadar gwamnati zuwa Daura a mako mai zuwa, Litinin, 29 ga Mayu.
Bankwana da FEC
Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ma za ta gudanar da taronta na bankwana a cikin mako mai zuwa.
Mambobin FEC sun haɗa da ministoci, masu magana da yawun shugaban ƙasa, shugaban ma’aikata da sauran manyan muƙamai da suka yi aiki tare da Buhari a lokacin mulkinsa.
Laccar ƙaddamarwa ta mai girma U. Kenyatta
A ranar Asabar 27 ga watan Mayu ne ake sa ran shugaba Buhari zai halarci taro, wanda tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta zai gabatar da laccar karɓar mulkin Tinubu mai taken “Deepening Democracy for Integration and Development” a Abuja.
Taron wani bangare ne na shirye-shiryen miƙa mulki.
Asali: Legit.ng