Na Rasa Gane Meyasa Amurka Ta Taya Bola Tinubu Murna, Atiku Abubakar
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna rashin jin daɗinsa da Sakataren Amurka ya kira Bola Tinubu ta waya
- Atiku, ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaben da ya wuce, ya ce matakin ya saɓa wa matsayar Amurka kan zaben shugaban Najeriya
- Ya ce yan Najeriya sun ɗora duk wata yarda da karfinsu kan kuri'unsu, abinda Amurka ta yi ta kar karya musu guiwa ne
Ɗan takarar shugaban ƙasa a babban zaben 2023 karkashin inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi mamakin yadda Sakataren Amurka ya kira zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ta wayar tarho.
Da yake martani kan lamarin a shafinsa na Tuwita, Atiku ya nuna takaicinsa a fili kan yadda ƙasar Amurka, uwa ga Demokaraɗiyya, ta aminta da zaben da ya baiwa Tinubu nasara.
"Tinubu Ba Zai Wuce Wata 6 Zuwa 7 a Kan Kujerar Shugaban Ƙasa Ba," Babban Jigo Ya Faɗi Abinda Zai Faru
A cewarsa, kiran da sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya yi wa Tinubu, tufka da warwara ne kan matsayar Amurka ta farko game da zaben shugaban kasan da aka kammala a Najeriya.
A kalaman da ya wallafa a shafinsa, tsohon mataimakin shugaɓan ƙasa, Atiku ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Na kasa yarda cewa Antony Blinken ya kira Tinubu, saɓanin matsayar Amurka ta farko kan zaɓen shugaba ƙasan Najeriya da aka kammala 2023."
"Babu wanda tunaninsa zai kawo masa haka duba da Amurka, wacce ake kallo a matsayin tushen Demokaraɗiyya, ta samu sahihin bayani kan gurbataccen zaɓen da ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023."
"Halatta zaben da kowa ya amince cike yake da almundahana a Najeriya ƙarya guiwa ne ga yan ƙasa, waɗanda suka ɗora yardarsu kacokan a kan kuri'unsu."
Idan baku manta ba, ranar Laraban nan da muke ciki, Blinken ya kira Bola Tinubu ta wayar salula, inda ya jaddada kudirin Amurka na ƙara yauƙaƙa dangantakarta da Najeriya.
Atiku Zai Karbi Najeriya Daga Hannun Tinubu Cikin Wata 6, Bwala
A wani rahoton na daban kun ji cewa Babban Jigon PDP ya ce zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ba zai wuce wata 6 zuwa 7 a kan gadon mulki ba.
Kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Daniel Bwala, ya bayyana abinda zai faru bayan wannan lokaci a Najeriya.
Asali: Legit.ng