Shugabancin Majalisa Ta 10: Ba A Yi Wa Yankin Arewa Adalci Ba a Tsarin Da Aka Zo Da Shi, Abdulaziz Yari

Shugabancin Majalisa Ta 10: Ba A Yi Wa Yankin Arewa Adalci Ba a Tsarin Da Aka Zo Da Shi, Abdulaziz Yari

  • Abdulaziz Yari, ya ce ba a yi adalci ga yankin Arewacin ƙasar nan ba idan aka miƙa manyan muƙaman gwamnati uku zuwa kudancin ƙasar
  • Jam’iyyar APC mai mulki, ta zaɓi Godswill Akpabio da Barau Jibrin a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa
  • Yari ya ce jam’iyyar APC takan tuntuɓi 'ya 'yanta kafin yanke hukunci, amma wannan karon ba ta yi hakan ba

Abuja - Zaɓaɓɓen sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma, Abdulaziz Yari, ya ce babu adalci ace an haɗa manyan kujerun gwamnati uku a kudancin Najeriya.

Yari ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Arise TV a ranar Talatar nan a Abuja.

Ya ce kamata ya yi jam’iyyar APC ta yi duba ya zuwa kowane yanki a lokacin da za ta bayyana sunayen shugabannin majalisar ta 10.

Kara karanta wannan

Kwamitin Aikace-Aikacen APC Na Ganawa Da Sanatoci Kan Matsalolin Da Suka Tunkaro Jam'iyyar

Yari Abu
Ba a Yi Wa Yankin Arewa Adalci Ba a Tsarin Da Aka Zo Da Shi, Cewar Abdulaziz Yari. Hoto: Solace Base
Asali: UGC

APC ta zaɓi Akpabio da Barau Jibrin a matsayin jagororin majalisa

Jam’iyya APC ta zaɓi Godswill Akpabio da kuma Barau Jibrin a matsayin shugaban majalisar da mataimakinsa a majalisar dattawa, The Cable ta yi rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yari dai na ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun sanatocin da suka gabatarwa da uwar jam'iyya takardar koke dangane da zaɓin shugabancin majalisar da ta yi.

A cewar yari:

"Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa dan Legas ne, alƙalin alƙalan Najeriya dan Oyo ne, kuma jam'iyyar APC ta tsayar da sanata daga Akwa Ibom a matsayin shugaban majalisar dattawa."
“Idan hakan ta faru, ya zamana ba a yi wa yankin arewacin Najeriya adalci ba."

Yari ya ƙara da cewa kamata ya yi jam’iyyar APC ta tuntuɓi duk masu ruwa da tsaki kafin yanke hukunci kan shugabancin majalisar.

Ya bayyana cewa jam'iyyar APC na da al'adar tuntuɓar 'ya 'yanta kafin yanke hukunci, amma wannan karon ba ta yi hakan ba.

Kara karanta wannan

Dan Majalisar APC Ya Hango Wani Babban Kuskure Da Jam'iyyar Za Ta Yi Kan Shugabancin Majalisa ta 10

Ya ce taro biyu kawai aka yi, sai aka bayyana musu sunayen waɗanda jam'iyyar ta zaɓa.

Jaridar Leadership ta ruwaito Yari na faɗar cewa tsarin da jam'iyyar APC ta yi ya saɓa da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, wanda ke magana kan raba dai-dai a tsakanin 'yan ƙasa.

Sanatocin APC sun yi ganawa ta gaggawa

A wani labarin da muka wallafa a baya, kwamitin aikace-aikace na jam'iyyar APC ya kira taron sanatoci aƙalla 40 don ganawa kan ɓarakar da ke neman kawowa jam'iyyar matsala.

Shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Adamu ne dai ya jagoranci taron da ya gudana a gidan Muhammadu Buhari da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng