Yan Majalisar Tsagin Adawa Sun Hakura da Neman Kakakin Majalisa Ta 10

Yan Majalisar Tsagin Adawa Sun Hakura da Neman Kakakin Majalisa Ta 10

  • Yan majalisun jam'iyyun adawa da suka lashi takobin kafa gwamnati a majalisa ta 10 sun yi amai sun lashe
  • Tawagar zababbun mambobin sun janye kudirinsu na neman kakaki da mataimakin kakaki
  • Tawagar ta ƙunshi yan majalisun tarayya na jam'iyyun PDP, NNPP, LP, ADC, YPP da kuma APGA

Zababbun mambobin majalisar wakilan tarayya na jam'iyyun adawa sun janye daga shirin neman takarar kakaki da mataimakin kakakin majalisa ta 10 gabanin rantsarwa ranar 5 ga watan Yuni.

Jaridar Punch ta tattaro cewa yan majalisun adawa sun yanke cewa ba zasu shiga tseren kujerun biyu ba saboda babu wani mamba daga cikinsu da ya nuna sha'awa.

Majalisar wakilai.
Yan Majalisar Tsagin Adawa Sun Hakura da Neman Kakakin Majalisa Ta 10 Hoto: HouseNGR
Asali: Twitter

Kakakin gamayyar yan majalisun adawa wacce suka raɗa wa, “Greater Majority," Honorabul Afam Ogene (LP-Anambra) ne ya bayyana janyewarsu a wurin wani taro a Abuja.

Kara karanta wannan

Sabuwar Rigima Ta Ɓalle a Jam'iyyar APC Kan Zaben Shugaban Kasa, Bayanai Sun Fito

Ya ce har zuwa karshen wa'adin da suka ɗibarwa batun, babu wani ɗan majalisa daga tsagin marasa rinjaye da ya nuna sha'awar tsayawa takarar manyan kujerun biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyun da suka haɗa wannan ƙungiya ta, “Greater Majority” sun haɗa da PDP, NNPP mai kayan marmari, Labour Party, SDP, ADC, YPP, da jam'iyyar APGA.

Da farko sun sha alwashin haɗa kai su tsayar da ɗan takara ɗaya, wanda zasu marawa baya ya zama kakakin majalisar wakilan tarayya ta 10.

Wane ɗan takara zasu goyi baya a yanzu bayan sun janye?

Honorabul Ogene ya ce tawagarsu ta gana da yan takarar da APC ta zaɓa kuma ga dukkan alamu sun cancanta. Ya kara da cewa ba zai faɗi abinda suka tattauna ba har sai kowane mamban tawagarsu ya samu bayani.

A rahoton Guardian, Ɗan majalisar ya ce:

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Abbas Da Kalu Sun Ziyarci Fitaccen Gwamnan APC, Sun Nemi Wata Muhimmiyar Alfarma 1

"Mun zauna da yan takarar da ke neman kujerar kakakin majalisa amma saboda bamu sanar da dukkan mambobinmu ba, ba zan faɗi bayanin abinda muka tattauna ba a yanzu."
"Ina mai tabbatar muku da cewa dukkan masu neman muƙaman sun cancanta a iya alamun da suka bayyana gare mu."

Shin dagaske ɗan takarar NNPP ya karbu kuɗi hannun gwamna Inuwa?

A wani labarin kuma Shugaban Masu Rinjaye ya fayyace gaskiya kan zargin ɗan takarar NNPP ya karbi kuɗi biliyan N2bn daga APC

Ɗan majalisar dokokin jihar Gombe ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa ɗan takarar jam'iyya mai kayan alatu ya karbi N2bn daga wurin ɗan takarar APC kafin zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262