Jerin Sunayen Shugabannin Majalisar Dattawar Najeriya Tun Daga 1999, Yankuna Da Jihohin Da Suka Fito
Rikicin shugabancin majalisa na ta ƙara kankama, musamman ma da jam'iyyar APC ta nuna daga yankunan da ta ke so shugabannin tagwayen majalisunta su fito.
Masana harkokin siyasa da dama, sun bayyana cewa kudu maso gabas ne yankin da ya fi dacewa ya fito da shugaban majalisar dattawa domin samun haɗin kai a ƙasa.
Sai dai jam'iyyar APC mai mulki, ta nuna ra'ayinta na bayyana Sanata Godswill Akpabio wanda ya fito daga yankin kudu maso kudu a matsayin wanda ta ke so ya shugabanci majalisar ta dattawa.
Tun dawowa mulkin dimokuraɗiyya a alif da ɗari tara da casa'in da tara (1999), yankin kudu maso kudu bai taɓa samar da shugaban majalisar dokoki ba tun daga farkon jamhuriya ta 4.
5 ɗin farko da aka yi daga 1999 sun fito ne daga kudu maso gabas, 2 da ke biye da su sun fito daga arewa ta tsakiya, a sa'ilin da na yanzu da ya gama ya fito daga arewa maso gabas. Legit.ng ta tattaro muku sunayen waɗanda suka shugabanci majalisar dokokin daga 1999 zuwa yau.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
1. Evan Enwerem
Enwerem ɗan asalin jihar Imo, shine shugaban majalisar dokokin na farko. Ya shugabanci majalisar dokokin a lokacin mulkin farar hula na tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, daga watan Yuni zuwa watan Nuwamban 1999.
2. Chuba Okadigbo
Okadigbo ya shugabanci majalisar dokokin daga 1999 zuwa 2000 shima a lokacin Olusegun Obasanjo.
Babban ɗan siyasa ne da ya fito daga jihar Anambra, ɗaya daga cikin jihohin kudu maso gabas.
3. Anyim Pius Anyim
Bayan tsige Okadigbo a shekara ta 2000, Pius Anyim ya jagoranci majalisar zuwa shekara ta 2003.
Pius ɗan asalin jihar Ebonyi, ya yi ta ƙoƙarin dawowa siyasa tun bayan barin kujerar shugabancin majalisar. Ko a shekarar 2022, Pius ya yi ƙoƙarin neman kujerar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar PDP.
4. Adolphus Wabara
Wabara ne ya jagoranci majalisar dokoki bayan Pius Anyim daga 2003 zuwa 2005.
Wabara ya fito ne daga jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya.
5. Ken Nnamani
Ken Nnamani ya fito ne daga jihar Enugu. ya jagoranci majalisar dattawan daga shekarar 2005 zuwa shekarar 2007.
6. David Mark
David Mark ya jagoranci majalisar dokokin na tsawon tenuwa ƙarƙashin mulkin Umaru Musa Yar'adua da kuma Goodluck Jonathan, wato daga 2007 zuwa 2015.
Mark ya fito ne daga jihar Benue, ɗaya daga cikin manyan jihohin arewa ta tsakiya.
7. Bukola Saraki
Abubakar Bukola Saraki, wanda shima daga yankin arewa ta tsakiya, ya jagoranci majalisar dokokin daga shekarar 2015 zuwa 2019.
Bukola saraki kafin zuwansa majalisa ya yi gwamnan jihar Kwara na tsawon tenuwa biyu.
8. Ahmed Lawan
Ahmed Lawan, ɗan asalin jihar Yobe da ke a Arewa maso Gabashin Najeriya ya kasance a majalisa tun 1999. Ya fara da majalisar wakilai ne kafin daga bisani ya koma majalisar dokoki.
Lawan ya jagoranci Majalisar Dattawa tun daga 2019 zuwa Yunin 2023.
9. Godswill Akpabio
Godswill Akpabio ya samu kuri'u 63 a zaben da aka gudanar a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, 2023 ya zama Shugaan Majalisa ya doke Sanata Yari wanda ya samu ƙuri'u 46.
Akpabio lauya ne masanin dokokin kasa kuma babban ɗan siyasa. Ya riƙe muƙamin Ministan Neja Delta daga 2019 zuwa 2022 karkashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Ya yi murabus daga kujerar Minista a ranar 11 ga watan Mayu, 2022 bisa umarnin Shugaban ƙasa na wancan lokacin Muhammadu Buhari don shiga takarar neman tikitin shugaban kasa a jam'iyyar APC.
Kafin haka Sanata Akpabio, ya yi gwamna jihar Akwa Ibom daga shekarar 2007 zuwa 2015.
Asali: Legit.ng