El-Rufai: Ba Zan Riƙa Zuwa Kaduna Ba Sai In Ta Kama Bayan Kammala Wa'adina
- El-Rufai ya bayyana cewa ko da za a ba shi muƙamin ministan Abuja ba ze karɓa ba domin shekarunsa sun wuce wurin
- Ya ce shi ko Kaduna ba ze riƙa zuwa ba in ya bar gidan gwamnati a 29 ga watan Mayu, sai dai in ya zama dole ne ya zo
- El-Rufai ya bayyana cewa yanzu shi fa ya girmi muƙamin ministan Abuja, don haka a nemi matasa masu jini a jika a basu
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa ba zai riƙa zuwa Kaduna ba har sai in ya zama dole bayan kammala wa'adin mulkinsa.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a Abuja, a wajen taron ƙaddamar da wani littafi a ranar Talata.
A rahoton The Cable, El-Rufai'n ya ce ba zai amshi kujerar Ministan Birnin Tarayya ba koda an bashi.

Source: UGC
Sai dai gwamnan bai bayyana cewa ko zai zamo ɗaya daga cikin waɗanda za a tafi da su a wannan gwamnati ko a'a ba, illa iyaka dai ya bayyana cewa ba zai karɓi kujerar ministan Abuja ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufai dai ya kasance shine tsohon ministan Abuja a lokacin tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, wanda a lokacinsa an yi manyan ayyuka, ciki kuwa hadda rushe-rushen manyan wurare a birnin.
Ni bana waigawa baya idan na wuce wuri, El-Rufai
A tabakin Gwamna El-Rufai:
“Na gama aiki na, na gama, bana waigawa baya. Tun da na bar birnin tarayya ban ƙara komawa ba sai a shekarar 2016, lokacin da aka bawa wani ɗan ajinmu a sakandire muƙamin minista.”
“Duk wani muƙami da na bari, ba na sake waiwayar shi, idan na bar Kaduna nan da kwanaki 19, ba zan riƙa ma zuwa ba sai in ya zama dole.”

Kara karanta wannan
Akwai Matsala: Jigon Jam'iyyar APC Ya Bayyana Abu 1 Da Ka Iya Kawo Cikas Ga Rantsar Da Tinubu
Ya ce a saboda haka ba ya wani tunani akan kujerar ministan birnin tarayya, wanda dalilin hakan ne ma ya sa baya sanyawa kowa baki a cikin ayyukan shi.
Ko da an bani mukamin ba zan karba ba, In ji gwamnan Kaduna El-Rufa'i
El-Rufai ya ƙara da cewa:
“Koda an bani muƙamin, to ba zan karɓa ba in tafi Abuja ba. Kamar yadda nace, ba na maimaita aji, kuma nasan matasa masu ɗanyan jini da zan iya turowa su yi aikin fiye da yadda na yi a lokacin ina ministan.”
“Shekaru na sun yi ma muƙamin yawa. Yanzu na girmi yin rusau, a samu matashi mai jini a jika ko matashiya a bata muƙamin.”
Buhari ya nemi a bashi damar karbo bashin $800m
Á wani labarin kuma, shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado ya aike da wata takarda majalisar dattawa yana rokonsu da su sahale masa ya karbo bashin kudade har $800m.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da bai wuce kwanaki 20 bane suka rage ma shugaban ya bar karagar mulki.
Asali: Legit.ng
