Majalisa Ta 10: Betara Ya Yi Fatali Da Umurnin APC, Ya Nuna Sha’awarsa Ta Tsayawa Takara
- Dan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Betara ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar majalisar wakilai ta 10
- Wannan na zuwa ne bayan da jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da jerin wadanda za su gaji wannan kujera ta majalisa
- Jam’iyyar APC ta tura shugabancin majalisar zuwa Arewa maso Yamma ya yin da Kudu maso Gabas ta dauki mataimaki
Abuja - Dan majalisar wakilai ta tarayya, Honarabul Mukhtar Aliyu Betara ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar majalisar wakilai ta 10, wanda ake sa ran za a kaddamar a watan Yuni mai zuwa.
Betara wanda shine shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin 8 ga watan Mayu a Abuja.
Taron wanda aka gudanar a Transcorp Hilton otal ya samu halartar mataimakin majalisar Honarabul Ahmed Wase da shugaban masu rinjaye na majalisar Honarabul Alhassan Ado Doguwa da Honarabul Sani Jaji da kuma Honarabul Tunji Olawuyi, cewar jaridar Tribune.
Zababben gwamnan Jihar Niger ya halarci taron
Sannan cikin wandanda suka halarci taron akwai zababben gwamnan jihar Niger, Honarabul Umaru Bago wanda shima dan majalisa ne mai ci kafun zabansa a matsayin gwamna, wanda ya kasance babban amininsa ne.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kwamitin tsare tsare na jam’iyyar APC a ranar Litinin 8 ga watan Mayu ta fitar da jerin masu gadon shugabancin majalisar, inda ta tura shugabancin zuwa Arewa maso Yamma yayin da mataimakin shugaban kuma Kudu maso Gabas.
Rahotanni sun tattaro cewa an zabi Hon Abbas Tajudden (APC-Kaduna) a matsayin wanda zai gaji Gbajabiamila a majalisa ta 10 yayin da mataimakinsa kuma shine Benjamin Kalu (APC-Abia).
Da yake maida martani, Betara ya ce ba abin da zai rage masa kwarin gwiwa na tsayawa takarar wannan kujera, yayin da ya yi mamakin yadda shugaban majalisar Honarabul Gbajabiamila ya zabi Honarabul Abbas duk da cewa akwai masu sha’awan wannan kujera da dama.
“In har a yau za a ce mataimakin majalisa na neman wannan kujera, shugaban kwamitin kasafin kudi ma na so, ga shugaban masu rinjaye shima yana so, to waye ne yafi cancanta a matsayi ya zama shugaban majalisa”, in ji shi.
Dalilin da yasa Arewa maso Yamma Suka Cacncanci Shugancin Majalisar Dattawa da Wakilai
A wani labarin, Honarabul Tajuddeen Abbas wanda yake sa ran zama shugaban majalisar wakilan tarayya ya bayanin dalilai na bai wa Arewa maso yamma fifiko a APC na shugabancin majalisa ta 10.
Ya yi wannan bayani ne a hirarsa da tashar Channels a ranar Lahadin da ta wuce, Honarabul Tajuddeen Abbas ya ce ba a banza ake ba Arewa maso Yamma muhimmanci ba.
Asali: Legit.ng