Majalisa Ta 10: Kungiyoyin Tinubu a Jihohin Arewa 19 Sun Tsayar Da Betara a Matsayin Kakakin Majalisa Na Gaba
- Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisa, Hon Aliyu Muktar Betara, ya samu gagarumin goyon baya kan kudirinsa na son zama kakakin majalisar wakilai na gaba
- Hakan ya kasance ne yayin da kungiyoyin goyon bayan Tinubu a jihohin arewa 19 suka lamuncewa Betara don darewa kujerar
- Kungiyoyin zababben shugaban kasar sun bayyana Betara a matsayin babban dan majalisa wanda ya fahimci lamuran da suka shafi kasa
Wasu gamayyar kungiyoyin goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a arewacin Najeriya sun tsayar da shugaban kwamitin kasafin kudi na majalsa, Hon. Aliyu Muktar Betara a matsayin kakakin majalisar wakilai ta 10.
Jagoran kungiyoyin, Kwamrad Abdullahi Bilal, ya ce Betara yana da gogewa, kwarewa, kuma mutum ne mai son hadin kan kasar, jaridar Daily Independent ta rahoto.
Kungiyoyin Tinubu a jihohin arewa 19 sun lamuncewa Betara, sun fadi dalili
Bilal ya kuma bayyana Betara a matsayin babban dan majalisa wanda ya fahimci lamuran da suka shafi kasa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kungiyoyin sun kara da cewa a matsayinsa na mai gudanar da aiki, Betara ya yarda da hada kan Najeriya da karfafa ta.
Kungiyoyin sun kuma ba da shawarar cewa a mika kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa da sakataren gwamnatin tarayya yankin arewa maso gabas da arewa ta tsakiyya, jaridar ThisDay ta rahoto.
Majalisa ta 10: Zaben ra'ayi ya nuna wanda zai iya zama kakakin majalisar wakilai na gaba
Shugaban kwamitin majalisa kan kasafin kudi, Hon. Aliyu Betara, ya bayyana a matsayin wanda aka fi so ya zama kakakin majalisa na gaba, a cewar wani zaben ra'ayinka.
A wani binciken Parliament Inc, jama'a sun bayyana Betara a matsayin wanda suke so ya gaji Femi Gbajabiamila a tsakanin sauran yan takara.
Zargin Kisan Kai: Doguwa Ya Shiga Matsala Yayin Da Kotu Ta Ba Atoni Janar Na Jihar Kano Sabon Umurni
A wata sanarwa da ya yi a ranar Juma'a, 28 ga watan Afrilu, kungiyar ta bayyana cewa dan majalisar na Borno shine babban zabin takwarorinsa.
Gwamnan jihar Kogi: Tinubu ya nuna goyon bayansa ga Usman Ododo
A wani labarin, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana goyon bayansa ga dan takarar jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Usman Ododo a zaben gwamnan jihar Kogi.
Gwamna Yahaya Bello ne ya gabatarwa Buhari da Ododo a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Juma'a, 28 ga watan Afrilu.
Asali: Legit.ng