Shugaban Kasa Mai Jiran Gado, Bola Tinubu, Ya Sa Labule da Shugaban APC
- Shugaban ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Tinubu, ya gana da shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu a Abuja
- Manyan jiga-jigan jam'iyya mai mulki sun halarci taro, ciki har da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan
- Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan Tinubu ya dawo Najeriya daga ƙasar Turai, inda ya huta tsawon wata ɗaya
Abuja - Zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya gana da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, a gidan da aka ware masa Defence House, Abuja.
Channels tv ta rahoto cewa daga cikin mahalarta taron, wanda ya gudana cikin sirri har da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan.
Sauran jiga-jigan da suka halarci taron sun ƙunshi, mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, Sakataren watsa labarai na APC ta ƙasa, Iyiola Omisore, da tsohon sakataren kwamitin kamfe, James Faleke.
Me suka tattauna a taron?
Jim kaɗan bayan karkare taron, shugaban jam'iyya mai mulki na kasa, Abdullahi Adamu, ya ce taron zama ne da aka saba na yau da kullum. Amma bai faɗi abinda suka tattauna ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wannan ganawa ta manyan masu faɗa aji a jam'iyyar APC mai mulki ya zo ne kwanaki biyu kacal bayan Tinubu ya dawo gida Najeriya daga ƙasar Faransa, inda ya shafe kusan wata ɗaya.
Nan da wata ɗaya da yan kwanaki, ake tsammanin za'a rantsar da zabbaben shughaan ƙasa a matsayin magajin shugaba Muhammadu Buhari, ranar 29 ga watan Mayu.
Tinubu ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaɓen shugaban kasan da aka kammala ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 kuma hukumar zabe INEC ta ayyana shi a matsayin zababben shugaban ƙasa.
Sai dai a halin yanzun manyan yan takara, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party sun ƙalubalanci nasarar Tinubu a gaban Kotu.
Allah ne kadai zai iya hana rantsar da Tinubu - Keyamo
A wani labarin kuma Ministan Buhari Ya Faɗi Wanda Zai Iya Hana Rantsar da Tinubu a Watan Mayu.
Ƙaramin Ministan kwadugo, Festus Keyamo, ya aike da sako mara daɗi ga tsagin Atiku, da sauran waɗanda suka shigar da ƙara gaban Kotu kan nasarar Tinubu.
Ya ce idan ba Allah ba, babu mahalukin da ya isa ya dakatar da rantsar da zababben shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng