Ganduje Ya Bukaci Magajinsa Da Ya Kammala Ayyukan Da Ba a Gama Ba a Kano
- Gwamna Abdullahi Ganduje ya bukaci magajinsa, Abba Kabir Yusuf da ya kammala ayyukan da gwamnatinsa ta bari wanda ba a kammala ba
- Ganduje ya ce shi bai riki kowa a zuciya ba kuma ya yafewa duk wanda ya yi masa laifi
- Ya jaddada muhimmancin kammala ayyukan da gwamnatinsa za ta bari domin amfanin mutanen jihar
Kano - Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa shi baya gaba da kowa yayin da zai bar kujerar mulki, yana mai bukatar magajinsa da ya kammala ayyukan da gwamnatinsa ta fara, Channels TV ta rahoto.
A wani sakon sallah da kwamishinan labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Muhammad Garba, ya saki a ranar Juma'a, 21 ga watan Afrilu, Ganduje ya nuna godiya ga Allah kan shekaru 20 da ya shafe a gwamnati.
Ya ce:
"Ina da dalili na godewa Allah da kuma tafiya ba tare da korafi kan kowa ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na yafewa wadanda suka yi mani laifi suma su yi koyi da hakan ta hanyar yafe mani."
Ganduje ya kuma roki daukacin al'ummar Musulmi da su yi koyi da darasin da suka koya a watan Ramadan wanda ya ke nuni ga soyayya da taimakon juna sannan ya yi kira ga addu'an zaman lafiya da ci gaba a jihar da ma kasar baki daya.
Ka kammala ayyukan da lokaci bai bari mun karasa ba, Ganduje ga Abba Gida-Gida
Gwamnan ya jaddada muhimmanci ci gaba a shugabanci sannan ya bukaci gwamnati mai zuwa da ta tabbatar da ganin cewa an kammala dukkanin ayyukan masu muhimmanci da aka aiwatar da kudaden masu biyan haraji.
"Babu wani aiki da aka aiwatar da kudaden masu biyan haraji da ya cancanci a yi watsi da shi," in ji shi.
Ya jaddada sakon Ganduje cewa gwamnan ba ya gaba da kowa kuma yana kira ga yafiya daga wadanda ya yi wa laifi a lokacin da yake shugabancin jihar.
Ya kara da cewar:
"Muna kira ga gwamnati mai zuwa da ta tabbatar da kammala dukkanin ayyuka masu muhimmanci da gwamnatinsa ta fara wanda lokaci ya hana kammala su saboda amfanin mutanen jihar."
A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa Abba Kabir Yusuf ya zargi Gwamna Abdullahi Ganduje da ware makudan kudade don daukar nauyin yan daba a lokacin cikon zaben yan majalisa da aka yi a ranar 15 ga watan Afrilu a jihar.
Asali: Legit.ng