29 Ga Watan Mayu: “Bana Tsoro, Yan Najeriya Za Su Kare Damokradiyya”, Buhari

29 Ga Watan Mayu: “Bana Tsoro, Yan Najeriya Za Su Kare Damokradiyya”, Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana da tabbacin yan Najeriya za su kare martabar damokradiyya ko bayan barinsa mulki
  • Buhari ya jadadda cewar zai mika mulki ga Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Afrilu
  • Shugaban Najeriyan ya ce yanzu yan Najeriya sun san lallai kuri'unsu na tasiri idan aka yi la'akari da gwamnoni da suka fadi zaben yan majalisar tarayya

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya hango kyakkyawar makoma tattare da damokradiyyar Najeriya, Vanguard.

Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai bayan sallar idi a Abuja, shugaban kasar ya ce ya yanke hukuncin ne bisa la'akari da yadda yan Najeriya ke kare damokradiyya duk da barazana.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
29 Ga Watan Mayu: “Bana Tsoro, Yan Najeriya Za Su Kare Damokradiyya”, Buhari Hoto: MBuhari
Asali: Twitter

Buhari ya ce:

"Yan Najeriya suna jin dadin dorewar damokradiyya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

“Na Matsu Na Koma Mahaifata Daura”: Inji Buhari Yayin da Ya Yi Bikin Sallah Na Karshe a Aso-Rock

"Sakamakon zaben 2023 wanda a ciki fiye da gwamnoni 10 suka sha kaye a kokarinsu na zuwa majalisar dattawa ya aika sako cewa yan Najeriya sun san karfin kuri'unsu da yadda za su yi amfani da su.
"Yan Najeriya na daraja damokradiyya. Sun nuna soyayyarsu gareta kuma za su kareta daga dukkan barazana.
"Za su ci gaba da zabe wanda ya danganta da abubuwan da suka fi so."

Zan mikawa sabuwar gwamnati mulki a ranar 29 ga watan Mayu, Buhari

Ya bayar da tabbacin cewa 29 ga watan Mayu na nan a matsayin ranar mika mulki ga sabuwar gwamnati, rahoton The Sun.

"Da izinin Allah, babu abun da zai hana mika mulki," ya bayar da tabbaci.

Kan shirye-shiryensa na barin mulki, shugaban kasar ya ce burinsa ya cika cewa Allah ya ba shi damar shugabancin wa'adi biyu na shekaru hudu-hudu sannan yana duba zuwa ga ranar mika mulki.

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Atiku Ya Fadi Abin da Yake Damunsa, Tinubu Ya Yi kira ga Musulmi

"Nagode Allah kan abun da ya yi mani da kuma abun da ya ba mu damar cimmawa.
"Ina duba zuwa ga ranar da zan koma garina, don na yi nesa da Abuja don shugaban kasa mai shigowa ya samu lokaci da sararin zartar da hukunci ba tare da na ja hankalinsa ba.

Na matsu na koma mahaifata ta Daura, Buhari

A gefe guda, shugaban kasa Buhari ya ce ya kagu ya bar mulki tare da komawa mahaifarsa a Daura, jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng