Zaben Adamawa: Kotu Ta Ki Sauraron Karar Da Binani Ta Shigar Gabanta

Zaben Adamawa: Kotu Ta Ki Sauraron Karar Da Binani Ta Shigar Gabanta

  • Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki sauraron karar da Sanata Aisha Dahiru Binani yar takarar gwamnan APC a jihar Adamawa ta shigar
  • An tattaro cewa an shigar da karar gaban babbar kotun tarayya a ranar Talata, 17 ga watan Afrilu
  • Bayan nazarin karar a tsanaki, Justis Iyang Ekwo ya ce kotun ba za ta sauraron shi ba saboda rashin rubutaciyyar takarda na hurumin yin haka

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta ki sauraron karar da yar takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa, Sanata Aisha Dahiru, wacce aka fi sani da Binani ta shigar a gabanta.

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa, Justis Ekwo, ya fada ma lauyan Sanata Binani, Mohammed Sheriff da ya gabatar da wata takarda da ta kotun hurumin sauraron karar ba akasin haka ba.

Kara karanta wannan

Kaico: Bashi ya yi mata katutu, ta siyar da jaririyarta mai watanni 18 kacal a wata jiha

Sanata Aisha Binani da Farfesa Mahmood Yakubu
Zaben Adamawa: Kotu Ta Ki Sauraron Karar Da Binani Ta Shigar Gabanta Hoto: INEC, Aisha Dahiru
Asali: Facebook

An tattaro cewa lauyan Gwamna Ahmadu Fintiri, Afeez Matomi, ya fada ma kotun cewa wanda yake wakilta zai bayyana a matsayin mutum na uku a karar.

Da Justis Ekwo ya tambaye shi ko an aike masu da takarda, Matomi ya bayyana cewa ba a yi masu aike ba amma sun shigar da wata bukata na neman kotu ta ki amsa bukatar Binani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matomi ya ce sun samu labarin shigar da wannan karar ne ta soshiyal midiya, don haka, suka yanke shawarar shigar da tasu bukatar.

Sai dai kuma Alkalin, wanda ya ki sauraron lauyan Fintiri, ya ce ya zama wajibi lauya ya bi abin da doka ta ce, rahoton Daily Trust.

Kotun da ke sauraron kararrakin zabe da kundin tsarin mulkin Najeriya ya kafa tana da hurumin bayyana wanda ya lashe zaben gwamna.

Binani ta ce bayan ayyanata a matsayin wacce ta lashe zabe, INEC ta kwace ikon kotun inda ta bayyana dawo da ita tare da soke hukuncin.

Kara karanta wannan

Sallah sai ranan Asabar: Ba za a ga wata ba a ranar Alhamis, masana sun fadi dalili

Alkalin ya dage shari'ar zuwa ranar Laraba, 26 ga watan Afrilu don ci gaba da sauraron lamarin.

Fintiri ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa, INEC

A gefe guda, mun ji cewa hukumar zabe ta INEC ta sanar da sakamakon zaben jihar Adamawa, inda tace Ahmad Fintiri ne ya lashe zaben a karo na biyu.

Hukumar zaben ta ce dan takarar PDP, Fintiri ya samu kuri'u 430,861 yayin da Aisha Dahiru Binani ta APC ta samu kuri'u 398,738.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng