Hukumar DSS Ta Shiga Aiki Kan Harin Da Aka Kaiwa Jami’inta a Jihar Adamawa
- Hukuma DSS ta magantu kan harin da wasu da ake zaton yan siyasa ne suka kaiwa jami'inta a Adamawa
- Rundunar tsaro ta farin kaya ta ce ta fara bincike a kan farmakin da aka kaiwa daya daga cikin jami'anta a jihar da ke arewa maso gabas
- Wani bidiyo ya yadu a soshiyal midiya inda aka gano wasu suna cin mutunci jami'in DSS yayin zaben cike gurbi a Adamawa
Rundunar tsaron farin kaya (DSS) ta ce ta kaddamar da wani bincike a kan harin da aka kaiwa daya daga cikin jami'anta a jihar Adamawa.
Rundunar tsaron sirrin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta saki a yammcin ranar Lahadi, 16 ga watan Afrilu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Source: UGC
Yadda aka ci zarafin wani jami'in DSS a yayin zaben gwamnan Adamawa

Kara karanta wannan
Daga karshe: Bayan dogon kai ruwa rana, Ado Doguwa ya lallasa dan tsagin Kwankwaso
An tattaro cewa an ci zarafin wani babban jami'in rundunar a lokacin zaben cike gurbi a jihar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An kuma nadi bidiyon wani jami'in DSS yayin da wasu mutane da ake zaton masu yi wa yan siyasa aiki ne suka ci zarafinsa.
Da yake martani ga jawabin, Peter Afunanya, kakakin DSS, ya ce:
"An ja hankalin rundunar tsaron farin kaya (DSS) zuwa ga wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya inda wasu makiran yan siyasa a jihar Adamawa suka ci mutuncin wani da ake zargin ma'aikacinta ne.
"Rundunar na burin sanar da jama'a cewa ta fara cikakken bincike a kan abubuwan da suka kai ga faruwar lamarin.
“Yayin da take kira da a kwantar da hankuli, rundunar ta kuma bukaci bangarorin da abin ya shafa a jihar Adamawa da su ci gaba da kasancewa masu son zaman lafiya tare da guje wa tashin hankali.”
Takaddama ya faru a zaben Adamawa

Kara karanta wannan
"Yan Sanda Na Kallo": Yan Daba Sun Sace Akwati Da Kayan Zabe Yayin Zaben Cike Gurbi A Katsina, Wakilin PDP
Da farko dai mun ji yadda Mista Hudu Ari, kwamishinan zaben jihar Adamawa, ya ayyana Sanata Aisha Dahiru Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar.
Kafin sanarwar tasa, Farfesa Mele Mohammed, baturen zaben, ya sanar da sakamakon kananan hukumomi 10 cikin 20 inda aka yi zaben cike gurbin.
INEC ta shiga lamarin sannan ta soke tsarin yayin da ta sammaci kwamishinan zaben da sauran jami'anta zuwa Abuja.
Asali: Legit.ng